Majalisar Dokokin Jihar Gombe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Majalisar Dokokin Jihar Gombe
unicameral legislature (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Jihar Gombe

Majalisar Dokokin jihar Gombe ita ce ɓangaren kafa doka na gwamnatin jihar Gombe ta Najeriya. Majalisar dokoki ce ta mambobi tare da mambobi guda 24 da aka zaba daga kananan hukumomi guda11 na jihar da aka ƙayyade zuwa mazaɓun jihohi guda 24. An ƙayyade ƙananan hukumomin da ke da yawan mabuƙata a mazaɓu biyu don ba da wakilci daidai. Wannan yasa adadin ƴan majalisar a majalisar dokokin jihar Gombe guda 24.

Ayyukan yau da kullun na Majalisar sune ƙirƙirar sabbin dokoki, gyara ko soke dokokin da ke akwai da kuma kula da zartarwa. An zaɓi membobin majalisar na tsawon shekaru hudu tare da 'yan majalisar tarayya (majalisar dattijai da ta wakilai). Majalisar jihar tana yin taro sau uku a mako (Talata, Laraba da Alhamis) a harabar majalisar a cikin babban birnin jihar, Gombe .

Shugabannin majalisar dokokin jihar Gombe ta shida sun haɗa da Abubakar Sadiq Ibrahim, shugaban majalisar (APC, yankin Yamaltu ta yamma) da Siddi Buba, mataimakin kakakin majalisar, (APC, Mazaɓar Kwami ta Yamma). Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) itace jam'iyya mafi rinjaye tare da kujeru guda19 yayin da People's Democratic Party (PDP) ke matsayin mara rinjaye inda take da kujeru 5 guda kacal.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]