Majalisar Shari'a ta Ƙasa (Najeriya)
Majalisar Shari'a ta Ƙasa | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
njc.gov.ng |
Majalisar shari’a ta kasa (NJC), ƙungiya ce ta zartaswa da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa bisa tanadin sashe na 153 na kundin tsarin mulkin ƙasar na shekara ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima domin kare ɓangaren shari’ar Najeriya daga son rai da son zuciya.[1][2][3][4]
Shugaban Majalisar shine Alkalin Alkalan Najeriya, Hon. Olukayode Ariwoola, yayin da mataimakin shugaban shine Hon Justice Musa Dattijo Muhammad, alkalin kotun koli . Sauran mambobin su ne: Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, Alkalan Kotun Koli hudu da suka yi ritaya, Shugaban Kotun ɗaukaka ƙara mai ritaya, Shugaban Kotun Masana’antu ta Kasa, Babban Alkalin Babban Kotun Tarayya, Babban Alkalin Babban Kotun FCT., Manyan Alkalan Babbar Kotun Jihohi hudu, Shugaban Kotun daukaka kara ta gargajiya, Grand Khadi na Kotun ɗaukaka karar Shari’a, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya, tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya, mambobin ƙungiyar lauyoyin Najeriya uku, da kuma Ma'aikatan Gwamnati biyu da suka yi ritaya. [4] Sakataren Majalisar na yanzu Ahmed Gambo Saleh, Esq. [4]
Ayyuka na doka
[gyara sashe | gyara masomin]Hukumar ta NJC tana gudanar da ayyukan shari’a da dama kamar baiwa shugaban Najeriya shawara da gwamnoni kan al’amuran da suka shafi shari’a. Suna kuma gudanar da ayyukan ladabtarwa tare da naɗawa da naɗa wakilan zartarwa a cikin shari'a.[5][6][7][8][9][10]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Kungiyar Benchers ta Najeriya
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "National Judicial Council - INFORMATION NIGERIA". informationng.com.
- ↑ "National Judicial Council Archives - Premium Times Nigeria". Premium Times Nigeria.
- ↑ Global Corruption Report 2007. 24 May 2007. ISBN 9781139465441.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 "National Judicial Council". www.njc.gov.ng. Archived from the original on 2020-10-09. Retrieved 2020-10-06. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "Jonathan Vs Salami: Why Adoke chose to play "the black sheep"". Vanguard News.
- ↑ "Salami: Jonathan Accepts NJC Recommendation, But..., Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 2015-04-28.
- ↑ "NJC Asks Jonathan to Re-instate Salami, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 2012-05-14.
- ↑ "National Judicial Council Sacks Three Rogue Judges". Pointblank News.
- ↑ "The Man Who Will Be Chief Justice of Nigeria, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 2014-11-29.
- ↑ "Nigeria's National Judicial Council 'Retires' Pension Thief Judge And Two Other Rogue Judges". Sahara Reporters.