Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Executive Council (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Nasarawa

Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa (wanda aka fi sani da, Nasarawa State Executive Council a Turance) ita ce mafi girman hukuma wacce take taka rawa a cikin Gwamnatin Jihar Nasarawa ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Nasarawa . Ta kunshi Mataimakin Gwamna, Sakataren Gwamnatin Jiha, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni waɗanda ke shugabantar sassan ma’aikatun, (tare da yardar bangaren majalisar dokoki na gwamnati) mataimakan na musamman na Gwamna.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Majalisar zartarwa ta wanzu don ba Gwamna shawara da jagorantar sa. Nadinsu a matsayin membobin Majalisar Zartarwa ya ba su ikon aiwatar da iko akan filayensu.

Jagoranci na yanzu[gyara sashe | gyara masomin]

Majalisar Zartarwa ta yanzu [1] tana aiki ne a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule wanda aka rantsar a matsayin Gwamna na 6 na Jihar Nasarawa a ranar 29 ga watan Mayu, shekara ta 2019. [2]

Ofishin Mai ci
Gwamna Abdullahi Sule
Mataimakin Gwamna Dr. Emmanuel Akabe
Sakataren Gwamnatin Jiha Muhammed Ubandoma-Aliyu
Shugaban Ma’aikatan Gwamnati Abari Aboki
Shugaban Ma’aikata
Sakataren dindindin, Gidan Gwamnati Hamza A. Gayam
Babban Sakatare Mai zaman kansa
Kwamishinan Noma da Albarkatun Ruwa Allananah O. Otaki
Kwamishinan Kudi, Kasafin Kudi, da Tsarin tattalin arziki Haruna Adamu Ogbole
Kwamishinan Kasuwanci, Masana'antu & Zuba Jari Boyi Obadiah
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya, da Fasaha Fati J. Sabo
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Kasa Musa I. Abubakar
Kwamishinan Lafiya Ahmed B. Yahaya
Kwamishinan yada labarai, Al'adu da yawon bude ido Dogo Shammah
Kwamishinan Shari'a Abdulkarim A. Kana
Kwamishinan Kasa da Ci gaban Birane Salihu LA Alizaga
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu Yusuf A. Turaki
Kwamishinan Ayyuka na Musamman Muhammad Abubakar Imam
Kwamishina mai kula da harkokin mata da cigaban al’umma Halima A. Jabiru
Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri Philip Dada
Kwamishinan cigaban matasa da wasanni Othman B. Adam

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-03-25. Retrieved 2020-10-15.
  2. http://dailypost.ng/2015/09/30/nasarawa-elections-maku-loses-bid-to-unseat-al-makura/