Makarantar Unguwar Zoma ta Jihar Jigawa
Makarantar Unguwar Zoma ta Jihar Jigawa | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | makaranta |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2010 |
nairaland.com… |
Makarantar unguwar zoma ta jihar Jigawa itace makarantar farko ta unguwar zoma a jihar Jigawa dake arewacin Najeriya.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An ƙirƙiro makarantar ne a watan Maris na 2010 kuma Aisha Moh'd Kazaure, wacce ungozoma ce kuma malama ta kafa, saboda karancin ungozomomi a jihar ta Jigawa. Tallafin ya fito ne daga Sashin Bunƙasa Kasashen rainon Burtaniya wanda ya amince da cewa, yayin da akwai mutane miliyan biyar da ke zaune a jihar, akwai ungozomomi kasa da 30. [1]
Shigarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ƴan mata za su iya shiga karatun idan suna da Takardun Ingilishi da Kimiyya. Waɗannan ƙananan ƙwarewa ne kamar yadda jahilcin mata ya wuce 90% a yankin. Ɗalibai yawanci mata ne kuma shekarunsu basu wuce ashirin [1] duk da cewa kashi 80% na ma’aikatan lafiya maza ne.
Sauran makarantu
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2015, Jihar Jigawa ta ce tana da niyyar kafa wata Makarantar ungozoma a Hadejia.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Called to be a midwife in northern Nigeria, UK Government, Retrieved 2 February 2016
- ↑ Jigawa to establish Nursing School, 29 July 2016, NGRGuardianNews, Retrieved 2 February 2016