Malika Zeghal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Malika Zeghal
Rayuwa
Haihuwa 1965 (58/59 shekaru)
ƙasa Tunisiya
Karatu
Makaranta École Normale Supérieure (en) Fassara
Sciences Po (en) Fassara
Thesis director Rémy Leveau (en) Fassara
Sana'a
Sana'a anthropologist (en) Fassara, political scientist (en) Fassara, sociologist (en) Fassara, Malami da malamin jami'a
Employers Jami'ar Harvard
University of Chicago (en) Fassara
Kyaututtuka

Malika Zeghal (an haife ta a shekara ta Alif (1965)[1] farfesa ce a Tunusiya a fannin Tunani da Rayuwar Musulunci ta Zamani a Jami'ar Harvard, kuma a da ta kasance mataimakiyar farfesa a fannin ilimin ɗan adam da ilimin zamantakewa na addini a Jami'ar Chicago Divinity School.[2]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kasance ɗaliba ta École Normale Supérieure kuma ta sami digiri na uku daga Institut d'Etudes Politiques de Paris a shekara ta Alif (1994). Ta fara binciken karatun digirinta a shekarar (1995) a Cibiyar Nazarin Gabas ta Hagop Kevorkian a Jami'ar New York kafin ta koma Faransa don shiga har tsawon shekaru goma, Cibiyar National de la recherche scientifique daga shekarun (1995) zuwa 2005.[3] Ita memba ce a Majalisar Kimiyya ta Cibiyar Kimiyya, Harrufa, da Fasaha ta Tunisiya.[4]

Aikinta, Gardiens de l'Islam, da aka rubuta da Faransanci bincike ne na tasirin malaman Jami'ar Al-Azhar. A. Marsot ta kafa hujja da tazarar ta na cewa: “Malaman Azhar sun yi imani da cewa aikinsu ne, da’awa, a matsayinsu na masu kula da addini su ga cewa dokokin ƙasa sun yi daidai da shari’a; don haka ake bayyana gwagwarmayarsu da hukuma. ta hanyar yin yunƙurin ajiye dokokin ƙasa a gefe domin shari’a”. [5] Littafin ya yi bayani ne kan yadda mu’amalar jihohi da malaman Azhari suka taimaka wajen bullowar sauran kungiyoyin Musulunci, wato ‘yan uwa Musulmi, a wajen cibiyoyin gargajiya.

Darussan Da Aka Koyar[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2013, ta koyar da wani kwas a Makarantar Divinity ta Jami'ar Harvard mai suna "HDS 3361: Political Islam in the 20th and 21st Centuries". [6]

Littattafai[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Malika ZEGHAL Archived 2006-11-28 at the Wayback Machine." Centre d'Études Interdisciplinaires des Faits Religieux.
  2. "Malika ZEGHAL Archived 2006-11-28 at the Wayback Machine." Centre d'Études Interdisciplinaires des Faits Religieux.
  3. "La Tunisienne Malika Zeghal nommée Professeur à Harvard". leaders (in Faransanci). Retrieved 2019-05-26.
  4. "Malika Zeghal". The Near Eastern Languages and Civilizations Department (in Turanci). Retrieved 2019-05-26.
  5. A. Marsot. Book Review: Gardiens de L'Islam. by Malika Zeghal. International Journal of Middle East Studies, Vol. 31, No. 2. (May 1999), pp. 283-284.
  6. Harvard Divinity School: Course Detail. HDS 3361 Political Islam in the 20th and 21st Centuries