Mamayewar Rasha a Ukraine na 2022

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Infotaula d'esdevenimentMamayewar Rasha a Ukraine na 2022
Последствия удара ракеты по Голосеевскому району киева (6).jpg
Iri yaƙi
military operation (en) Fassara
military offensive (en) Fassara
invasion (en) Fassara
attempt (en) Fassara de short victorious war (en) Fassara
Bangare na Russo-Ukrainian War (en) Fassara
Kwanan watan kalanda 2022
Time period (en) Fassara Russia under Vladimir Putin (en) Fassara, contemporary history (en) Fassara da Shmyhal Government (en) Fassara
Wuri Ukraniya
Ƙasa Ukraniya, Luhansk People's Republic (en) Fassara, Donetsk People's Republic (en) Fassara, Rasha da Belarus
Participant (en) Fassara
Sanadi Charter of the United Nations (en) Fassara
Yana haddasa government and intergovernmental reactions to the 2022 Russian invasion of Ukraine (en) Fassara
2022 Ukrainian refugee crisis (en) Fassara
economic impact of the 2022 Russian invasion of Ukraine (en) Fassara
solidarity concerts for Ukraine (en) Fassara
Adadin waɗanda suka rasu 24,000
Hanyar isar da saƙo
Chronology (en) Fassara
Siege of Mariupol (en) Fassara
Bucha massacre (en) Fassara
Has part or parts (en) Fassara
Eastern Ukraine offensive (en) Fassara
Southern Ukraine offensive (en) Fassara
Northeastern Ukraine offensive (en) Fassara
Hashtag (en) Fassara #StandWithUkraine, #StayWithUkraine, #RussiaInvadedUkraine, #StopRussianAggression, #UkraineUnderAttack, #UkraineInvasion, #BanRussiaFromSWIFT, #CloseTheSky, #SendNATOtoUkraine, #UAразом, #ShelterUkrainianSky, #StopPutin, #StopPutler, #WWIII, #WW3, #PutlerKaput, #WorldForUkraine, #UkraineRussiaWar, #UkraineRussianWar, #StopPutinNOW, #RussianUkrainianWar, #UkraineWar, #PutinWarCrimes, #StopRussia, #FightForUkraine, #FreeSky, #RussianInvasion, #WarInUkraine, #RussiaUkraineWar, #RussiaWarOnUkraine, #PutinIsaWarCriminal, #ZaPobedu, #СвоихНеБросаем, #ZaРоссию, #МЫВМЕСТЕ, #cancelrussianculture, #TheTaken, #RussianCultureKills, #PutPutinOnTrial, #StandUpForUkraine, #SendPutinToJupiter, #UnitedWithUkraine da #ArmUkraineNow

A ranar 24 ga Fabrairu, 2022, Rasha ta ƙaddamar da wani gagarumin farmaki a Ukraine, maƙwabciyarta ta kudu maso yammacin ƙasar, wanda hakan ke nuna ruruwar cigaban yaƙin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine tun daga shekara ta 2014. Sakamakon ƴanci da Ukraine ta samu na zama da kanta a shekarar 2014, wannan yaƙin an ayyana shi a matsayin mafi girman tashin hankali da ba'a taɓa gani ba a turai tun bayan yaƙin duniya. Akan kalli sanadin amatsayin Rasha tana son haramtawa Ukraine shiga ƙungiyar NATO bisa doka,[1] ƙawancen ƙasashen Turai tare da Amurka da Kanada. Kafin kai farmakin sai da Rasha ta amince da wasu jihohin Ukraine guda biyu da suka ayyana kansu amatsayin yan tattun ƙasashe, wato Jamhuriyar Jama'ar Donetsk da Jamhuriyar Jama'ar Luhansk, sannan kuma sojojin Rasha suka fara mamaye yankin Donbas na gabashin Ukraine a ranar 21 ga watan Fabrairu, 2022.

Da misalin ƙarfe 03:00 UTC (06:00 Moscow Time, MSK) a ranar 24 ga Fabrairu, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bada sanarwar wani farmakin soji a gabashin Ukraine; mintuna kaɗan bayan haka, aka fara kai hare-haren manyan makamai a wurare daban-daban a cikin biranen ƙasar musamman ma wajajen jami'an tsaron ƙasar, ciki har da babban birnin kasar Kyiv da ke arewacin ƙasar. Hukumar kula da kan iyakokin Ukraine ta bayyana cewa an kai wa kan iyakokinta da Rasha da Belarus hari.[2][3] Bayan sa'o'i biyu, sojojin kasa sun shiga da misalin karfe 05:00 UTC.[1] Ƙasashe da dama sun yi tir da harin tare da sanyawa Rasha takunkumi.[4]

Vladimir Putin a lokacin da aka bayyana harin
Abubuwan da ke faruwa a Gabashin Ukraine a lokacin mamayewa
An lalata tsarin da makami mai linzami

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Why is Russia invading Ukraine and what does Putin want?". BBC News (in Turanci). 24 February 2022. Archived from the original on 19 December 2021. Retrieved 24 February 2022.
  2. "Russia attacks Ukraine". CNN. 24 February 2022. Archived from the original on 24 February 2022. Retrieved 24 February 2022.
  3. "Украинские пограничники сообщили об атаке границы со стороны России и Белоруссии". Interfax. 24 February 2022. Archived from the original on 24 February 2022. Retrieved 24 February 2022.
  4. Morin, Rebecca (24 February 2022). "World leaders condemn Russian invasion of Ukraine; EU promises 'harshest' sanctions – live updates". USA Today. Archived from the original on 24 February 2022. Retrieved 24 February 2022.