Jump to content

Mariama Sylla

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mariama Sylla
Rayuwa
Haihuwa Dakar
ƙasa Senegal
Ƴan uwa
Ahali Khady Sylla
Sana'a
Sana'a darakta da mai tsara fim
IMDb nm1501809

Mariama Sylla Faye ta kasance darakta, Jaruma, mawaƙiya 'yar asalin ƙasar Senegal.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Mariama Sylla an haife ta ne a Dakar kuma ƙanwar marubuciya ce kuma mai shirya fim Khady Sylla.[1][2] Mahaifiyarta tana aiki a ofishin sinima, kuma Sylla ta zama mai sha'awar fim din tun tana 'yar shekara bakwai, saboda ana nuna fina-finai da yawa a farfajiyar dangi.[3] a cikin 1996 ta samu diploma a École supérieure d'art dramatique de Genève. Sylla ta fara sana'a a matsayin ma gabatarwa a ɗakin taro wanda aka sani da (Theate) cikin harshen faransanci a Switzerland. Tana gudanar da aikin gabatarwar a ƙarƙashin jagorancin Claude Stratz, Charles Joris, Dominique Catton, Gilles Laubert, Raoul Pastor, Philippe Mentha, da kuma Georges Guerreiro.[4]

Sylla ta kafa kamfanin kera Guiss Guiss Communication a shekara ta 2003. Ta ba da umarnin gajeriyar fim din Dakar Deuk Raw a shekara ta 2008, wacce ta yi nazari kan tsohuwar kabilar Lesbous da ke Dakar. A cikin shekara ta 2010, Sylla ta jagoranci bada umarni a shirin fim na Skirmisher Marc Gueye: My Pen, My Fight, shirin fim ɗin yana nuna wani haziƙin tsohon soja na Farkon a yaƙin Indochina. Bugu da ƙari tana ɗaura murya a shirye-shiryen rediyo da talabijin.[4]

Sylla ta kasance a matsayin darakta a cikin fim din 2014 Une simple parole tare da 'yar uwarta Khady, kuma ta gama shi lokacin da Khady ta mutu. Fim ɗin yana nazarin al'adar bayar da labarai a Senegal kuma ya sami Lambar Bambancin daga Nunin Fina-Finan Duniya da Talabijin na Mata.[5]

  • 2004 : Welcome to Switzerland (actress, as Amelia)
  • 2005 : Derrière le silence (director)
  • 2006 : Hors Série (director)
  • 2008 : Tierra roja (short film, actress)
  • 2008 : Dakar Deuk Raw (short film, director)
  • 2010 : Skirmisher Marc Gueye: My Pen, My Fight (director)
  • 2014 : Une simple parole (co-director)
  • 2017-2019 : Quartier des banques (TV series, actress)

Sylla ta auri ɗan jarida Modou Mamoune Faye.

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Mariama Sylla". Festival Scope. Retrieved 16 November 2020.
  2. "Une Fenêtre ouverte & Le Monologue de la muette". Centre Wallonie-Bruxelles (in French). Archived from the original on 17 November 2020. Retrieved 16 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  3. "Mariama Sylla Faye". Africultures (in French). Retrieved 16 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  4. 4.0 4.1 "Mariama Sylla". Hors Surface (in French). Archived from the original on 24 October 2020. Retrieved 16 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  5. "Mariama Sylla". Theatre Online (in French). Retrieved 16 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)