Masallacin Iran, Bur Dubai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masallacin Iran, Bur Dubai
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaTaraiyar larabawa
Haɗaɗɗiyar daular larabawaDubai
BirniDubai (birni)
Coordinates 25°16′N 55°17′E / 25.26°N 55.29°E / 25.26; 55.29
Map
Karatun Gine-gine
Style (en) Fassara architecture of Iran (en) Fassara

Masallacin Iran Hosainia [lower-alpha 1] masallacin 'yan Shi'a ne Hosainia da ke kusa da tsohon Textile Souk a gundumar Bur Dubai ta Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.[1] Masallacin kuma ana kiransa da "Masallacin Ali Ibn Abi Talib " wanda shi ne babban jigon shi'a.[2][3] An fara gina masallacin a shekara ta 1979.[4]

Tsarin ginin[gyara sashe | gyara masomin]

Masallaci Iran, a Bur Dubai

Masallacin yana da kamanni daga gine-ginen Farisa kuma ya shahara saboda kyawunsa na waje da ciki. Yana da fasalillika da suka haɗa da; facade, onion dome, faience da kuma shuɗin kalar shuɗin azure wanda ke cikin sifofin furanni.[5] An rubuta rubutun Musulunci daga Alqur'ani a cikin furanni masu launin kore, rawaya, ja da fari. Masallacin ya samo asali ne a tsakanin al'ummar Iran mazauna birnin.[5]

Lonely Planet ya kwatanta a masallacin a matsayin "masallaci mai sauƙi amma mai ban mamaki a cikin yanki na Bur Dubai Souq" kuma sananne ne saboda; hasumiyoyi da sauran abubuwan masallacin."[6]

Akwai wani masallacin Iran a Satwa wanda shi ma masallacin ‘yan Shi’a ne da aka yi masa fasalin abubuwa makamancin haka.[5]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Bayanan kula[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Larabci: الحسينية الشيعية الايرانية‎; {{|حسينية شیعه ایرانی‎}}

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Bur Dubai, Textile Souk, outside Iranian Mosque". Dubai360. Archived from the original on 6 January 2021. Retrieved 1 July 2015.
  2. "Ali Ibn Abi Talib Mosque | Dubai | United Arab Emirates | AFAR". www.afar.com. 2020-06-17. Retrieved 2021-08-31.
  3. "Profiles: Key Individuals in the Shia-Sunni Divide". NPR.org (in Turanci). Retrieved 2021-08-31.
  4. kbshaji (2014-03-22). "Iranian Mosque Dubai - Imam Hossein Mosque, Dubai, UAE - Jumeirah". DubaiTravelator.com - Dubai travel and tourism directory links - Dubai Hotel car rental booking links (in Turanci). Retrieved 2021-08-31.
  5. 5.0 5.1 5.2 Thomas, Gavin (2003). Frommer's Dubai and Abu Dhabi Day by Day. John Wiley & Sons. p. 43. ISBN 9780470684597. Retrieved 2 July 2015.
  6. Planet, Lonely. "Must see attractions Dubai, United Arab Emirates". Lonely Planet.