Masarautar Bazin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Bazin

Wuri
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 9 century
Rushewa 9 century

Masarautar Bazin wata masarauta ce ta farko wacce take a arewa maso gabashin Afirka. A cewar Al-Yaqubi, tana ɗaya daga cikin gwamnatocin Beja guda shida da suka wanzu a yankin a karni na 9. Yankin masarautar yana tsakanin Aswan da Massawa.[1]

Yawancin jama'ar 'yan asalin Kunama ne, da ake kira "Bazin" (ko wani lokacin Baden, Bazen da dai sauransu), waɗanda suke yin addinin gargajiya. Mutanen Bazin sun kasance karkashin kariyar daular Abyssiniya.[2] An bayyana wannan a cikin abin da ake kira Dutsen Ezana,  inda aka ce wani Sarkin Aksumite da ba a bayyana sunansa ba ya kare Bazin daga mamaye Noba. Da rugujewar Masarautar Aksum a kusan shekara ta 700 AD, dangin Beja sun mamaye kuma suka kafa masarautu da dama a Eritrea ta yau, ciki har da Bazin.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Elzein, Intisar Soghayroun (2004). Islamic Archaeology in the Sudan . Archaeopress. p. 13. ISBN 1841716391 . Retrieved 3 March 2015.
  2. Elzein, Intisar Soghayroun (2004). Islamic Archaeology in the Sudan . Archaeopress. p. 13. ISBN 1841716391 . Retrieved 3 March 2015.