Masarautar Bida
Masarautar Bida | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jihohin Najeriya | Jihar Neja | ||||
Babban birni | Bida | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Ƙirƙira | 1531 | ||||
Rushewa | 1856 |
Masarautar Bida masarauta ce ta gargajiya a Najeriya, wacce ta gaji tsohuwar Masarautar Nupe, tare da hedkwatarta a Bida, Jihar Neja. Shugaban ƙasar shi ne Etsu Nupe, wanda aka ɗauka a matsayin shugaban mutanen Nupe.
Tarihin masarautar
[gyara sashe | gyara masomin]An kafa tsohuwar Masarautar Nupe a tsakiyar karni na 15 a cikin wani kwari tsakanin kogin Neja da Kaduna a yankin da ke tsakiyar Najeriya a yanzu. Tarihin farko yafi dogara ne da tatsuniyoyin da aka watsa ta hanyar magana. Sarki Jibiri, wanda yayi sarauta a wajajen 1770, shine sarki Nupe na farko daya fara musulunta. Etsu Ma’azu ya kawo masarautar a lokacin da take kan mulki mafi girma, ya mutu a 1818. A wannan lokacin Fulani suna samun iko a duk Arewacin Najeriya. Bayan rasuwar Ma’azu da kuma yayin yaƙe-yaƙe masu zuwa masarautar Nupe ta zama ƙarƙashin masarautar Gwandu. Masaba, dan shugaban Fulanin Mallam Dendo kuma mahaifiyarsa 'yar Nupe, ya sami mulki a shekarar 1841 Har zuwa yau wannan masarautar tana bikin ranar al'adun ta da aka sani da Ranar Al'adun Nupe, don tunawa da shan kaye ga sarakunan Ingila a yankin su a wancan karnin.
Sarakunan
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]https://web.archive.org/web/20110211233553/http://www.nyscbida.5u.com/nupe-history.htm https://web.archive.org/web/20110211233321/http://www.nyscbida.5u.com/emirate-origin.htm http://www.worldstatesmen.org/Nigeria_native.html https://doi.org/10.4314%2Fafrrev.v11i3.2