Jump to content

Masarautar Jabriyya: Zamanin Sarki Ajwad bin Zamil (Littafi)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Masarautar Jabriyya (a Larabce: السلطنة الجبرية: عهد السلطان أجود بن زامل) littafi ne wanda marubuci dan kasar Qatar Ali bin Ghanim Al-hajir ya rabuta a shekara ta 2018. Ya rubuta littafinne akan rayuwar sarki Ajwad bin Zamil, wanda yayi mulki a gabashin tsibirin larabawa a karkashin masarautar Jabariyya. [1]

Kunshiya[gyara sashe | gyara masomin]

Littafin ya maida hankali akan rayuwar sarki Ajwad bin Zamil wanda ya rayu daga shekara ta 1418 zuwa 1496 Miladiyya sannan ya shafe fiye da shekaru 26 akan karagar mulki. Littafin na kunshe da abinda ya shafi rayuwar sarkin ta fuskar halayyanshi, da kuma ci gaban da ya kawo a zamaninshi. Za a iya kasa littafin zuwa kashi hudu:[2]

  1. Shimfida akan tarihin zamanin mulkin Jabriyya
  2. Rayuwar sarki Ajwada da hawarsa kan karagar mulki: wannan bangare na dauke da Tsarin mulkin sarki Ajwad bin Zamil irin siyasar da sarki Ajwad ya gudanar, da kuma yankunan da ke karkashin ikonshi wanda suka hada da Qatar, da Oman da kuma Baharen
  3. Tsarin siyasar cikin gida da waje: wannan bangare ya kunshi tsarin soji da kuma yanayin zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da ya samu a zamanin sarki Ajwad bin Zamil. Yana kuma dauke da alaqa da kuma qawance dake tsakanin sarki Ajwad da sauran sarakunan yankin larabawa da Indiya da Arewacin Afirka.
  4. fadada masarautar Jabriyya a yankin Najd da Oman: wannan yayi bayani ne akan fadadawa da wannan masarauta ta samu a yankin Najd da kuma Oman tare da ci gaban ta kawo ma yankunan.
  5. Fadada masarautar Jabriyya ta yankin Qatar da Baharen da Qaten: Yana dauke da bayanin fadada masarautar Jabriyya karkashin mulkin Ajwad musamman a yankunan Qatar da Bahren da Qatef.

Kana iya duba[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. علي بن غانم الهاجري (2018): السلطنة الجبرية: عهد السلطان أجود بن زامل دار جامعة حمد بن خليفة للنشر
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-09-15. Retrieved 2022-09-15.