Masarautar Sarki Kothi
Masarautar Sarki Kothi | |
---|---|
Wuri | |
Dominion of the British Empire (en) | Dominion of India (en) |
Jihar Indiya | Hyderabad State (en) |
Megacity (en) | Hyderabad |
Coordinates | 17°23′34″N 78°28′51″E / 17.392802°N 78.4808343°E |
History and use | |
Ƙaddamarwa | 1911 |
Mai-iko | Nizam of Hyderabad (en) |
Karatun Gine-gine | |
Zanen gini | Kamal Khan (en) |
|
Fadar Sarki Kothi ko Fadar Nazri Bagh fadar sarauta ce a Hyderabad, Telangana, dake a Indiya. Ita ce fadar da tsohon mai mulkin Jihar Hyderabad, Sir Mir Osman Ali Khan, Nizam na Bakwai, ke zaune. Fada ce da mahaifinsa Mahboob Ali Pasha ya saya, wanda yake da sha'awar siyan gidaje masu ban sha'awa.[1][2]
Asali
[gyara sashe | gyara masomin]Tun farko dai wannan babbar fada mallakin wani mai martaba ne, wanda ake kira da Kamal Khan wanda aka taƙaita rubuta sunayensa daga (Kamal Khan ) zuwa ‘KK’ an rubuta KK akan dukkan kayan ɗaki, ƙofofi, kayan abinci, tagogi, da ma kan gandayen karfe na fadar. Mahboob Ali Pasha yayi sha'awar mallakar fadar amma ƙaƙƙarfan zane-zane na baƙaƙe ya sa shi ɗan taka tsantsan. Don samarwa kansa mafita, wani mai shari'a ya fito da kyakkyawar mafita. Ya bada shawarar tunda can dama gidan ana kiransa da yaren Urdu da "Kothi" kuma zai iya zamowa itace fadar sarki, za'a iya sake sanya mata suna da "King Kothi" don a daidaita tsarin farko. Nizam ya ji daɗi, sai ya yi gaba ya sayi fada. Ta haka ne aka samu sunan fadar "Sarki Kothi" (King Kothi).
Tun-tale-tale (Tarihi)
[gyara sashe | gyara masomin]Kamal Khan ne ya gina fadar, kuma ya sayar da ita ga Nizam yayin da ya bayyana yana son fadar. Nizam ya shiga fadar lokacin yana matashi wato yanada shekara 23 kacal a rayuwarsa. Bayan ɗarewarsa akan karagar mulki a shekarar 1911, ya ci gaba da zama a fadar, bai koma fadar Chowmahalla inda mahaifinsa ke yake rayuwarsa.
A cikin fadar da ke bazuwa, an ajiye kayayyaki masu tsada iri-iri a cikin kurtuttukan (mazubi, kurtu ɗaya jam'insa kuma kututtuka) ƙarfe, an kulle su da kwaɗuna waɗanda akayi a Engila. Fadar tana da manyan gine-gine guda uku, wanda aka kasu kashi biyu. Hakanan akwai babban ɗakin karatu wanda Nizam na ƙarshe yayi amfani dashi.
Ɓangaren gabas na rabin fadar, wanda yanzu ke karkashin wani asibitin gwamnatin jihar, Nizam ne ke amfani da shi don ayyukan gwamnatinsa da biki. Daga rabinta a yammaci, wanda yanzu ke da katanga, yana da manyan gine-ginen zama da aka fi sani da Nazri Bagh ko Mubarak Mansion kuma har yanzu mallakar Nizam ne mai zaman kansa.
Babban ƙofar Nazri Bagh koyaushe tana da labule da aka lulluɓe ta dashi, shiyasa aka fi sanin ta da ƙofar purdah. Lokacin da Nizam ya fita daga fada, akan ɗaga purdah don nuna cewa sarki baya gida. Rundanar Maisaram, ƴan sanda da sojojin Sarf-e-Khas ne ke gadin ƙofar. Nizam cigaba da zama a nan har zuwa mutuwarsa a shekarar 1967.
Gine-ginen Fadar
[gyara sashe | gyara masomin]Fadar tana da manya manyan ƙofofin shiga da ginshiƙai, da katakai a kan tagogi masu rufi, da ƙaton falo a ƙofar shiga.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "No takers for Nazri Bagh Palace". The Times of India. Archived from the original on 5 November 2012. Retrieved 7 March 2012.
- ↑ Bhavani, Divya Kala (2017-05-31). "Fading Palatial Facade". The Hindu (in Turanci). ISSN 0971-751X. Retrieved 2019-02-06.