Jump to content

Matsalolin muhalli a Mali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Matsalolin muhalli a Mali
aspect in a geographic region (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Abubuwan da suka shafi muhalli
Facet of (en) Fassara Abubuwan da suka shafi muhalli
Ƙasa Mali
Taswiran Mali a zane

Abubuwan da suka shafi muhalli a Mali, sun haɗa da kwararruwar hamada, Sare Dazuka, zaizayar ƙasa, fari, da rashin wadataccen ruwan sha. Sare dazuzzuka matsala ce ta musamman kuma mai girma. A cewar ma'aikatar muhalli, al'ummar ƙasar Mali na cin ton miliyan 6 na itace a duk shekara domin yin katako da kuma man fetur. Domin biyan wannan buƙata, ana yin asarar murabba'in kilomita 4,000 a duk shekara, wanda kusan ke tabbatar da lalacewar gandun daji na ƙasar.

Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka shafi muhalli a Mali shi ne kwararowar hamada. Ƙasar Mali ta faɗa cikin fari shekaru da dama a yanzu kuma hakan yana shafar ƙasar. Zaizayar ƙasa, sare dazuzzuka, da asarar wuraren kiwo, duk manyan matsaloli ne a Mali. Mali kuma tana da ƙarancin ruwa.[1]

Don taimakawa wajen ɗorewar matsalar da ke ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar Mali gwamnati ta ware kashi 3.7 cikin 100 na ɗaukacin yankin ƙasar ta Mali. Ta amince da yarjejeniyoyin muhalli na ƙasa da ƙasa da suka shafi bambancin halittu, sauyin yanayi, kwararowar hamada, nau'ukan da ke cikin haɗari, da kuma kariya ta fuskar ozone . [2]

A cewar hukumar ta FAO, kashi 10.2% ko kuma kusan hekta 12,490,000 na ƙasar Mali na da dazuzzuka. Mali tana da dajin da aka shuka hekta 530,000. Canjin dazuzzukan : Tsakanin shekarar 1990 da ta 2010, Mali ta yi asarar matsakaicin ha 79,100 ko kuma 0.56% a kowace shekara, jimilla ta yi hasarar 11.2%, ko kuma kusan 1,582,000 ha, a wannan lokacin. Ƙasar Mali tana da maki 7.16/10 a shekarar 2018, inda take matsayi na 51 a duniya cikin kasashe 172.[3]

Canjin yanayi

[gyara sashe | gyara masomin]
Hasashen canjin yanayin zafi a Mali, 1901 zuwa 2020.

Ko da yake Mali ba ta ba da gudummawa sosai ga hayakin iskar gas a duniya ba (GHG), tana cikin jerin ƙasashen da suka fi fuskantar sauyin yanayi. [4] Sauyin yanayi na ƙaruwar duka da tsanani da yawaitar ambaliya da fari a ƙasar da kuma yiwuwar afkuwar bala'o'in yanayi. [4] Hakanan yana iya yin illa ga samar da abinci da cututtuka, kuma yana ƙara raunin zamantakewa tsakanin mazauna ƙasar. [4]

  • Namun daji na Mali
  • Rally for Education about Sustainable Development, jam'iyyar siyasa
  1. "Mali- Environment." Encyclopedia of The Nations. N.p., n.d. Web. 16 May 2013
  2. "Land and Resources, Environmental Issues." countries quest. N.p., n.d. Web. 17 May 20.
  3. Grantham, H. S.; Duncan, A.; Evans, T. D.; Jones, K. R.; Beyer, H. L.; Schuster, R.; Walston, J.; Ray, J. C.; Robinson, J. G.; Callow, M.; Clements, T.; Costa, H. M.; DeGemmis, A.; Elsen, P. R.; Ervin, J.; Franco, P.; Goldman, E.; Goetz, S.; Hansen, A.; Hofsvang, E.; Jantz, P.; Jupiter, S.; Kang, A.; Langhammer, P.; Laurance, W. F.; Lieberman, S.; Linkie, M.; Malhi, Y.; Maxwell, S.; Mendez, M.; Mittermeier, R.; Murray, N. J.; Possingham, H.; Radachowsky, J.; Saatchi, S.; Samper, C.; Silverman, J.; Shapiro, A.; Strassburg, B.; Stevens, T.; Stokes, E.; Taylor, R.; Tear, T.; Tizard, R.; Venter, O.; Visconti, P.; Wang, S.; Watson, J. E. M. (2020). "Anthropogenic modification of forests means only 40% of remaining forests have high ecosystem integrity - Supplementary Material". Nature Communications. 11 (1). doi:10.1038/s41467-020-19493-3. ISSN 2041-1723.
  4. 4.0 4.1 4.2 Badal, Lionel (2021-12-09). "Mali in the Frontlines of Climate Change - Our World". Our World: United Nations University. Retrieved 2021-07-13.