Mazarkwaila

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Raken Mazarkwaila

Mazarkwaila wata narkarkiyar sukari ce da ake hada ta da rake, ita wannan sukari ana hada ta ne a yan kunar karkara, sannan tana da mutuqar amfani a jikin dan Adam.

Mazarkwaila ko rawar doki akan kira ta dashi.

Mazarkwaila ita ce sukari ta ainihin tun kafin zuwan sukari na zamani(Sugar).Rawar doki ko mazarkwaila akan haɗa wannan narkarkiyar sukari da rake sannan akan sami tsohon doki zai dinga kaɗa wannan inji sannan asamu ruwan rake, sai a dafa shi sosai har takai da anyi mazarkwaila.sannan a sanya shi a murfi bayan ya sha iska sai a kama hanyar kasuwa domin sai dawa.

Kasar da akafi samu wannan sukari babu kamar ƙasar Kaduna, a yankin ƙaramar hukumar Makarfi da yan kunna kamar jahar Kano.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]