Mazdak
Mazdak | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 5 century |
Mutuwa | 529 (Gregorian) |
Yanayin mutuwa | hukuncin kisa |
Malamai | Zaradust-e Khuragen (en) |
Sana'a | |
Sana'a | mai falsafa da ɗan siyasa |
Imani | |
Addini | Zoroastra |
Mazdak (ya mutu 524 ko 528) ya kasance mai kawo canji ne daga Farisa kuma mai rajin neman addini. Ya zama mai tasiri a ƙarƙashin mulkin Sassaniyya Shahanshah Kavadh I. Ya yi da'awar shi annabin Allah ne, kuma ya fara mallakar jama'a da shirye-shiryen jin daɗin jama'a.
Mazdakiyanci
[gyara sashe | gyara masomin]Shi ne babban wakili na tsarin koyarwar addini da ilimin halittar rayuwa da ake kira Mazdaki, wanda ake ganinsa a matsayin sabon fasalin addinin Zoroastra . [1] [2] Wasu mutane sunyi jayayya, koyarwarsa tana nuna tasiri daga Manichaeism kuma. Zoroastra shine babban addinin Sassaniyya a Persia. Mazdak firist na Zoroastrian ne. Yawancin limaman addinan Zoroastra suna ɗaukar koyarwarsa a matsayin bidi'a .
Akwai bayanai kadan a game da Mazdakism. Koyarwar Khurramism ta samo asali ne daga Mazdakism kuma ana iya amfani da shi wajen faɗa ma wasu bayanai game da Mazdakism. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Yarshater, Ehsan. 1983. The Cambridge history of Iran, volume 2. p.995-997
- ↑ Shaki, Mansour. 1985. The cosmogonical and cosmological teachings of Mazdak. Papers in Honour of Professor Mary Boyce, Acta Iranica 25, Leiden, 1985, pp. 527-43.
- ↑ Yarshater, Ehsan. The Cambridge history of Iran, volume 2.