Michael Ede

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

     

Michael Maigeri Ede (an haife shi a ranar 3 ga watan Maris 1975) shi wakilin na 'yan ƙwallon ƙafa na Najeriya ɗan Burtaniya, marubuci kuma ɗan kasuwa. [1] Shi mai shiga tsakani ne mai rijista da Hukumar Kwallon Kafa (FA) a Burtaniya. Shi ne wanda ya kafa Uplift11 Sports - hukumar wasanni da ke wakilta da shiga tsakani a madadin 'yan wasan kwallon kafa da masu horaswa. [2] Littafinsa na farko, One Shot, ya harhada mukalolinsa, wadanda ya gabatar, wadanda kuma kamfanin, Maple Publishers ne ya buga su a ranar 3 ga Maris 2023. [3] An bayyana One Shot a cikin Vanguard a matsayin "cikakken dan jagora domin samun nasarar a kasuwancin zamani." Littafin ya zama a matsayin wanda ya fi ciniki a manhajar Amazon a Amurka, Kanada, Australia da kuma United Kingdom.

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

Ede da ne ga Honourable John Ede, dan majalisar dattawa a majalisar dokokin Najeriya ta biyu da kuma Awidi Ede mahaifiyarsa. An haife shi kuma ya girma a Najeriya kafin ya wuce zuwa Ingila don kammala karatunsa da kuma kula da iyalinsa a Burtaniya.

Ede ya halarci Jami'ar Jos ta Najeriya kuma ya sami digiri na farko a fannin Kimiyyar Halittu . Daga nan ya koma kasar Ingila domin kara karatu inda ya sami digiri na biyu a fannin kasuwanci (MBA) a Makarantar Kasuwancin Manchester Metropolitan University . [4] [5] Kwarewarsa daga MBA a cikin 2011 ya kasance a kan tsara dabarun kasuwanci da kuma kasuwancin kasuwancin kasa da kasa.

Bayan kammala karatun digirinsa na biyu sai Ede ya soma ayyuka da wadansu kamfanoni daga ciki har da HSBC da Barclays da Capgemini da WiPro Technologies da Bank of Ireland da AstraZeneca . Har ila yau, karatunsa ya taimaka masa ya wajen yin suna a cikin masana'antar kwamfuta (IT) da kuma zaburar da shi wajen kafa kamfanin tuntuɓar dangane da ayyukan kwamfuta da gudanarwa a cikin 2013, mai suna Maigmike Consulting. [6] Ede ya kuma sami takardar shedar kasancewa ƙwararren Wakilin Kwallon Kafa daga John Viola Academy kuma ya kammala karbar horo na zaben 'yan wasa masu daraja ta da S4 Scouting Professional Football Recruitment, a Ingila. [6] [7] An bayyana Ede a cikin wallafe-wallafe da yawa, ciki har da Forbes, Guardian, Vanguard, New Telegraph, ThisDay, <i id="mwhg">The Sun</i> Nigeria da sauransu.

Daga karshe dai a cikin shekarar 2020, Ede ya aza harsashin samar da hukumar don Wasannin Uplift11 - hukumar kula da wasanni. Wannan kamfani ya zama incubator wanda ke cike gibi tsakanin hazaka da dama ga waɗancan 'yan wasan da ba su da kayan aiki. [6]

manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :13
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :1
  3. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :7
  4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :6
  5. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :5
  6. 6.0 6.1 6.2 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0
  7. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :10