Mirza Ghiyas Beg
Appearance
Mirza Ghiyas Beg | |||
---|---|---|---|
Mayu 1611 - 1622 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Qazvin (en) , 16 century | ||
ƙasa | Iran | ||
Mutuwa | Kangra (en) , 1622 | ||
Makwanci |
Tomb of I'timād-ud-Daulah (en) Agra | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Asmat Begum (en) | ||
Yara |
view
| ||
Karatu | |||
Harsuna | Farisawa | ||
Sana'a |
Mirza Ghiyas Beg (Farisawa: میرزا غیاث بیگ) Wanda kuma aka sani da sunan I'timad-ud-Daula (Farisawa: اعتماد الدوله)[1] Shi babban ɗan siyasa ne a Daular Mughal wanda ya ɗauki matsayin Vakīl-i-Mutlaq na Daular Mughal, watau Firayim Minista, daga shekara ta 1611 miladiyya zuwa shekara ta 1622 miladiyya. Ya kasance fitaccen jami’in gwamnati, wanda ‘ya’yansa mata da jikokinsa suka auri sarakuna. Shi ne mahaifin Nur Jahan, matar sarki Jahangir, kuma mahaifin Abul Hasan Asif Khan, wazir-e 'azam, kuma kakan Mumtaz Mahal, shahararriyar sarauniya, matar sarki Shah Jahan.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Pant 1978, p. 4