Momee Gombe
Momee Gombe | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Gombe, 1999 (25/26 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Maimuna Abubakar (An haife ta a ranar 11 ga watan Yulin, shekara ta alif ɗari tara da casa'in da tara(1999). wacce aka fi sani da Momee Gombe, 'yar wasan Kannywood ce.[1][2][3].
Rayuwa da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Momee Gombe a ranar 11 ga watan Yulin, shekara ta alif dari Tara da casa'in da tara 1999, a garin Gombe, Gombe State Nigeria. Ta yi makarantar firamari da sakandari a Garin Gombe.[4][5].
Momee Gombe, kamar yadda aka fi kiranta da shi, ta girma da sha’awar yin fim. Sai dai kuma ta zama nakasasshe a harkar fim sakamakon aurenta kafin burinta ya cika. Bayan mutuwar aurenta sai ta koma masana’antar kai tsaye. Momee ta ambaci mai shirya fina -finan Kannywood Auwal Mu'azu a matsayin mutumin da ya taimaka mata ta shiga Masana'antar Kannywood. Da farko an san ta da rawa, Tana taka rawa mai kayatarwa masu kallo wanda ake upload
a YouTube da sauran shafukan sada zumunta. Jarumar ta fito tare da fitattun mawakan Hausa da jarumin Fina -finan Adam A Zango wanda ta ambata a matsayin mai ba ta shawara a masana'antar Kannywood, sai mashahurin mawaƙi Hamisu Breaker, da mawaƙi kuma ɗan wasa Garzali Miko da sauran matasa mawaƙan Hausa a Arewacin Najeriya.[6][7].
Fina-finai
[gyara sashe | gyara masomin]Ta fito a fina -finai sama da guda 30, daga cikinsu akwai:
- Kishin Mata
- Asalin Kauna.
- Sarki goma
- Zainabu Abu
- Alaqa series
- Gidan sarauta
[tps://naijadrop.com/download-mome-gmbe-so-duniya-mp3-song-audio-video So Duniya (Song)] Archived 2022-02-12 at the Wayback Machine
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Momee tayi aure ta rabu da maigidanta.sannan tana da ɗiya ɗaya.[8][9][10].
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Cikakken Tarihin Momee Gombe » Kundin tarihi". Kundin tarihi (in Turanci). 2021-03-28. Archived from the original on 2021-09-07. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ "Takaitaccen Tarihin Jaruma Momee Gombe." Alummar Hausa (in Turanci). 2020-10-15. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ . "Meet Momee Gombe Whose Marriage Ended In Less Than 30 Days". Sahara News Watch (in Turanci). 2020-09-13. Archived from the original on 2021-09-07. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ "Jaruma Momee Gombe (Maimunah Abubakar)". Haskenews-All About Arewa. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ "Meet Kannywood Actress Maimuna Abubakar Biography Career And Pictures". Sahara News Watch (in Turanci). 2020-06-26. Archived from the original on 2021-09-07. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ "Upcoming Kannywood actress Maimuna Abubakar Biography, Career Pictures and more". Wothappen (in Turanci). 2020-10-23. Archived from the original on 2021-09-07. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ Odogwu (2021-02-02). "Momee Gombe Biography, Age, Career, And Phone Number". NaijaDailys (in Turanci). Archived from the original on 2021-04-20. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ "Momee Gombe Explains How Her Marriage Ended In 30 Days - Opera News". ng.opera.news. Archived from the original on 2021-09-07. Retrieved 2021-09-07.
- ↑ Askira, Aliyu (2020-10-16). "I didn't terminate my marriage because of Hamisu Breaker – Momee Gombe". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2021-09-07.
- ↑ "Momee Gombe Has Debunked Claims of Her Birthing Daughter, Explains Genesis of the Rumours - Opera News". ng.opera.news. Archived from the original on 2021-09-07. Retrieved 2021-09-07.