Moscow Cathedral Mosque

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Moscow Cathedral Mosque
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaRasha
Capital of Russia (en) FassaraMoscow
Coordinates 55°46′45″N 37°37′37″E / 55.7792°N 37.6269°E / 55.7792; 37.6269
Map
History and use
Opening2015
Maximum capacity (en) Fassara 10,000
Karatun Gine-gine
Yawan fili 18,900 m²
Replaces former Moscow Cathedral Mosque (en) Fassara
Offical website
Masallacin Cathedral mai tarihi da aka kewaye da ginin sabon masallacin (2009)
Babban zauren Masallacin

Babban Masallacin Moscow ( Russian: Московская соборная мечеть , Moskovskaya sobornaya mechet ) babban Masallacin birnin Moscow ne na Kasar Rasha. Yana kan titin Olimpiysky, kusa da filin wasa na Olympic a tsakiyar birnin Moscow din.

Tarihin Masallacin[gyara sashe | gyara masomin]

An gina ainihin tsarin Masallacin a shekara ta 1904 bisa ga yadda mai zane-zanen tsarin gine-ginen watoNikolay Zhukov ya tsara Mana, kuma an sake yin wasu gyare-gyare tun lokacin. Ana kuma kiran Masallacin da "Masallacin Tatar" saboda mafi yawan jama'ar da ke cikinsa sun fito ne daga kabilar Tatar. A Masallacin na Juma'a dake a Moscow, ana kuma ganin shi a matsayin babban masallacin ƙasar Rasha. Yana ɗaya daga cikin masallatai hudu dake a birnin Moscow.[1]

An rushe tsohon ginin Masallacin a ranar 11 ga Satumba, 2011. Shawarar ruguza shi ta ya jawo cece-kuce. A watan Yunin shekarar 2008, an san masallacin a matsayin wani abu na al'adun gargajiya, da gado, duk da haka, a karshen 2008 an cire shi daga jerin abubuwan tarihi da na gine-gine. Don haka, a lokacin rushewar, babu yadda za'ayi a hana rushe shi. Akwai shirye-shiryen sake gina Masallacin, kuma masanin tsarin gine-gine Ilyas Tazhiyev ne ya tsara aikin ginin. Daya daga cikin dalilan sake gina ginin shi ne, ginin ya karkata da digiri da dama daga hanyar zuwa Makka. Aikin ya hada da tarwatsa masallacin, tare da tattara dukkan duwatsun, sannan a sake hada shi tare da saka daidaita tsarin fuskar shi. Amma a shekara ta 2009, Majalisar Muftis ta kori Tazhiyev, da farko ta yi ikirarin sake yin wani aikin sake gina ginin, sannan kuma ta ruguza ginin da cewa ya kusa rugujewa. Tazhiyev ya bayyana bayan rushe Masallacin cewa har yanzu ana iya sake gina ginin, kuma ginin bai kusa rugujewa ba.

Masallacin Cathedral na Moscow ya zama ginin addini na farko da aka rushe a birnin Moscow tun shekara ta 1978.

Sabon Ginin Masallacin[gyara sashe | gyara masomin]

An gina sabon Masallaci a wurin da aka gina na da din. An kaddamar da shi a hukumance a ranar 23 ga Satumba, shekarar 2015. Ginin Masallacin da aka jaddada yana daukar 10,000, sabon Masallacin kenan mutane dubu goma na iya taruwa suyi Sallah a cikin Masallacin. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya da Mahmoud Abbas na Falasdinu tare da shugabannin musulmin yankin ne suka halarci bikin bude wannan masallaci.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Krainova, Natalya (13 September 2011). "Historic Mosque Demolished on 9/11 Anniversary". The Moscow Times. Retrieved 4 July 2016.