Mosobila Kpamma
![]() | |||
---|---|---|---|
1 Oktoba 1969 - 13 ga Janairu, 1972 District: Talensi Constituency (en) ![]() Election: 1969 Ghanaian parliamentary election (en) ![]() | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 1934 (90/91 shekaru) | ||
ƙasa | Ghana | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Tamale College of Education certificate (en) ![]() | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Malami da ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Progress Party (mul) ![]() |
Mosobila Kpamma ɗan siyasan Ghana ne kuma memba a majalisar dokoki ta farko a jamhuriya ta biyu ta Ghana mai wakiltar mazaɓar Talensi-Nabdam a yankin Upper Ghana a ƙarƙashin memba na Progess Party (PP).[1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mosobila a shekarar 1934. Ya halarci kwalejin horar da malamai ta Tamale. inda ya sami Takardar Horon Malamai daga baya kuma ya yi aiki a matsayin malami kafin ya shiga Majalisa.
Ayyuka da Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Kpamma yayi aiki a matsayin malami kafin shiga siyasa. Ya fara harkokin siyasa ne a shekarar 1969 lokacin da ya zama ɗan takarar majalisar dokoki don wakiltar mazaɓar sa Talensi-Nabdam a yankin Upper Ghana kafin a fara zaɓen majalisar dokokin ƙasar ta Ghana a shekarata 1969 .
An rantsar da shi a majalisar farko ta Jamhuriya ta Biyu ta Ghana a ranar 1 ga Oktoban shekarar 1969, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen Ghana na shekarar 1969 da aka gudanar a ranar 26 ga Agusta 1969. kuma wa’adin mulkinsa ya ƙare a ranar 13 ga Janairun shekarata 1972.
Rayuwar mutum
[gyara sashe | gyara masomin]Ya kasance shugaba a garinsu, Kirista cikin imani.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ghana Year Book (in Turanci). Daily Graphic. 1971.