Jump to content

Mougins

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mougins


Wuri
Map
 43°36′00″N 6°59′41″E / 43.6°N 6.9947°E / 43.6; 6.9947
Ƴantacciyar ƙasaFaransa
Administrative territorial entity of France (en) FassaraMetropolitan France (en) Fassara
Region of France (en) FassaraProvence-Alpes-Côte d'Azur (en) Fassara
Department of France (en) FassaraAlpes-Maritimes (en) Fassara
Arrondissement of France (en) Fassaraarrondissement of Grasse (en) Fassara
Canton of France (en) Fassaracanton of Mougins (en) Fassara
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 19,677 (2021)
• Yawan mutane 767.43 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Located in statistical territorial entity (en) Fassara Q108921304 Fassara
Q3551094 Fassara
Yawan fili 25.64 km²
Altitude (en) Fassara 760 m
Sun raba iyaka da
Tsarin Siyasa
• Mayor of Mougins (en) Fassara Richard Galy (en) Fassara (18 Mayu 2020)
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 06250
Kasancewa a yanki na lokaci
Wasu abun

Yanar gizo mougins.fr
Twitter: villedemougins Instagram: villedemougins LinkedIn: mairiedemougins Edit the value on Wikidata
Notre-Dame de Vie Chapel a Mougins a lokacin rani
Majalisar birnin Mougins 2008-2014.
Mougins Vogelperspektive.

Mougins ( French: [muʒɛ̃] ; Occitan [muˈʒis] ; Latin [muːˈɡiːnũː] ) wata ƙungiya ce dake a sashin Alpes-Maritimes a yankin Provence-Alpes-Côte d'Azur daga kudu maso gabashin Faransa. Ya zuwa shekarata 2019, tana da yawan jama'a kimanin mutum dubu goma sha tara da dari tara da tamanin da biyu 19,982.

Tana kan tsaunukan Cannes, a gundumar Grasse. Mougins tana da nisa mintuna 15 a tafiyar mota daga Cannes. Garin yana kewaye da dazuzzuka, musamman dajin Valmasque. [1] A cikin garin akwai itatuwan pine, zaitun da bishiyar cypress.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Mutane na rayuwa a tudun Mougins tun kafin zamanin Rumawa. Ƙabilun Ligurian na da waɗanda suka zauna a bakin teku tsakanin Provence da Tuscany, sun kasance daga ƙarshe sun hade da Daular Roma sannan kuma sun zama wani ɓangare na gwamnatin Ligurian na hukuma wanda Sarkin sarakuna Augustus (X Regio) ya kirkiro. A kan hanyar Aurelia ta haɗa Roma zuwa Arles, Muginum ya fara wanzuwa ne ƙarni na 1 BC.

A cikin 1056, Gillaume de Gauceron, Count of Antibes, ya ba Mougins tsaunin ga Sufaye na Malaman Honorat (daga kusa da Îles de Lerins kusa da bakin tekun Cannes) wadanda suka ci gaba da gudanar da ƙauyen, kuma har zuwa jajibirin Juyin juya hali na Faransa a 1789 tarihinsa yayi daidai da na Abbey. Tsohon gidan kotun sufaye, ɗakin da aka ɓoye wanda yanzu ake kira "Salle des Moines" ("Dakin Sufaye") yana kan bene na farko na gidan abincin L'Amandier .

An gina shi da tsawon mita 260 a sama, an karawa ƙauyen kariya a tsakiyar zamani. Sifarsa ta karkace, ginshiƙanta da ƙofofinta guda uku, waɗanda har yanzu Porte Sarrazine (Ƙofar Sarrazine) ce kawai ke wanzuwa a yau, kofar ya bada kariya mai mahimmanci duk da yawan hare-haren lokacin yaƙi a tsawon tarihinta. Ƙauyen ya girma har zuwa wajen ainhin iyakarta, yayin da yake ci gaba da bin tsarin zagaye na ainihin tsarinta.

A lokacin Yaƙin Nasara na Austriya na ƙarni na 18, sojojin Austro-Sardinia sun kai hari a ƙauyen kuma sun kone ta da wuta. Bayan haka, an sake gina wasu ginshiƙan tare da gina wasu ƙananan titunan gidaje na farkon ƙarni na 19.

Alkaluma[gyara sashe | gyara masomin]

Historical population
YearPop.±%
17931,330—    
18001,500+12.8%
18061,538+2.5%
18211,724+12.1%
18311,962+13.8%
18361,883−4.0%
18411,918+1.9%
18461,828−4.7%
18511,831+0.2%
18561,805−1.4%
18611,752−2.9%
18661,677−4.3%
18721,652−1.5%
18761,694+2.5%
18811,678−0.9%
18861,581−5.8%
18911,548−2.1%
18961,657+7.0%
19011,599−3.5%
19061,541−3.6%
19111,770+14.9%
19211,800+1.7%
19262,800+55.6%
19313,400+21.4%
19363,270−3.8%
19463,210−1.8%
19543,851+20.0%
19625,274+37.0%
19686,346+20.3%
19758,492+33.8%
198210,197+20.1%
199013,014+27.6%
199916,051+23.3%
200719,906+24.0%
201217,884−10.2%
201719,473+8.9%

Tattalin Arziki[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin ƙarni na 19 da farkon karni na 20, ƙauyen ya kasance cibiyar samar da furanni, yana samar da lavender, wardi da jasmine don turare a yankin Grasse na kusa. Mougins ƙauye ne mai albarka, inda duka tsoffin gine-gine da gidajen ƙarni na 19 ke nan kamar yadda aka gina su.

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Makarantar Mougins, sunan da aka fi amfani da shi na makarantar shine Makarantara kasa da kasa ta Mougins British International School tana gudana tun lokacin da aka kafa ta a 1964. Akwai makarantar firamare "les cabrieres" da makarantar taka-tsaki "les campelieres".

Masu unguwanni[gyara sashe | gyara masomin]

Shaida F. Tajasque Lavabre-Delanoy Jacques Sauvan André Bailet Georges Pellegrin Roger Duhalde Richard Gali
Lokaci 1904- 1930-1941 1945-1961 1961-1970 1970-1977 1977-2001 2001-2024
Jam'iyyar siyasa Gaullist RPR UMP

Tagwaye birane[gyara sashe | gyara masomin]

An haɗa Mougins tare da:

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Communes na sashen Alpes-Maritimes
  • Bernard Lancret
  • Johann Michael Rottmayr
  • Pablo Picasso

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "La Valmasque", mougins.fr (in French).

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

Wikimedia Commons on Mougins  

Samfuri:Alpes-Maritimes communes