Jump to content

Pablo Picasso

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Pablo Picasso
Murya
director of Museo del Prado (en) Fassara

Rayuwa
Cikakken suna Pablo Diego José Francisco de Paula Juan Nepomuceno María de los Remedios Cipriano de la Santísima Trinidad Ruiz y Picasso
Haihuwa Malaga, 25 Oktoba 1881
ƙasa Ispaniya
Mazauni Château of Vauvenarg (en) Fassara
Mas Notre-Dame-de-Vie de Mougins (en) Fassara
rue des Grands-Augustins (en) Fassara
Harshen uwa Yaren Sifen
Mutuwa Mas Notre-Dame-de-Vie de Mougins (en) Fassara da Mougins, 8 ga Afirilu, 1973
Makwanci Château of Vauvenarg (en) Fassara
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (pulmonary edema (en) Fassara
Gazawar zuciya)
Ƴan uwa
Mahaifi José Ruiz Blanco
Mahaifiya Maria Picasso
Abokiyar zama Olha Khokhlova (en) Fassara  (12 ga Yuli, 1918 -  11 ga Faburairu, 1955)
Jacqueline Roque (mul) Fassara  (2 ga Maris, 1961 -  8 ga Afirilu, 1973)
Ma'aurata Nusch Éluard (en) Fassara
Dora Maar (mul) Fassara
Fernande Olivier (mul) Fassara
Marie-Thérèse Walter (mul) Fassara
Françoise Gilot (mul) Fassara
Eva Gouel (mul) Fassara
Yara
Ahali Lola Ruiz Picasso (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Makaranta Escola de Arte e Superior de Deseño Pablo Picasso (en) Fassara
Royal Academy of Fine Arts of San Fernando (en) Fassara
(1897 -
Harsuna Catalan (en) Fassara
Faransanci
Yaren Sifen
Malamai José Ruiz Blanco (en) Fassara
Isidoro Brocos (en) Fassara
Antonio Muñoz Degrain (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a painter (en) Fassara, Mai sassakawa, mai zanen hoto, printmaker (en) Fassara, Mai tsara rayeraye, ceramicist (en) Fassara, poster artist (en) Fassara, illustrator (en) Fassara, mai daukar hoto, Mai zana kaya, designer (en) Fassara, jewelry designer (en) Fassara, mai zane-zanen hoto, architectural draftsperson (en) Fassara, muralist (en) Fassara, assemblage artist (en) Fassara, collagist (en) Fassara, mai tsara bangarorin fim, drawer (en) Fassara, marubin wasannin kwaykwayo, mai zane-zane da masu kirkira
Wurin aiki Faris, Royan (en) Fassara, Aix-en-Provence (en) Fassara, Avignon, Antibes (en) Fassara, Schoorl (en) Fassara, A Coruña (mul) Fassara, Barcelona da Madrid
Muhimman ayyuka Guernica (en) Fassara
Les Demoiselles d'Avignon (en) Fassara
Chicago Picasso (en) Fassara
Three Musicians (en) Fassara
Science and Charity (en) Fassara
Garçon à la pipe (en) Fassara
Massacre in Korea (en) Fassara
Kyaututtuka
Wanda ya ja hankalinsa Henri Rousseau (mul) Fassara, Paul Cézanne (mul) Fassara, Sassaka a Africa da Maria Prymachenko (en) Fassara
Mamba Academy of Arts of the GDR (en) Fassara
Accademia delle Arti del Disegno (en) Fassara
Fafutuka Cubism (en) Fassara
surrealism (en) Fassara
post-impressionism (en) Fassara
Sunan mahaifi Pau de Gósol
Artistic movement graphics (en) Fassara
ceramic (en) Fassara
figurative art (en) Fassara
self-portrait (en) Fassara
Hoto (Portrait)
nude (en) Fassara
figure (en) Fassara
history painting (en) Fassara
mythological painting (en) Fassara
allegory (en) Fassara
animal art (en) Fassara
abstract art (en) Fassara
landscape painting (en) Fassara
marine art (en) Fassara
still life (en) Fassara
vanitas (en) Fassara
Imani
Addini mulhidanci
lapsed Catholic (en) Fassara
Jam'iyar siyasa French Communist Party (en) Fassara
IMDb nm0681444
Hoton picasso
Picasso da modigliano da salomon

Pablo Picasso mai fenti ne. Picasso an haife shi a Malaga (yanzu Hispania) a shekara ta 1881, ya mutu a Mougins (Faransa) a shekara ta 1973. Ya kasance mai zane dan kasar Sipaniya, mai sassake-sassake, masanin gidan wasan kwaikwayo wanda ya kwashe mafi yawan rayuwarsa a kasar Faransa. Ya kasance daya daga cikin masu zane da suka shahara a ƙarni na 20. Yayi fice na musamman ta salon zanensa da ya kirkiri na “Cubism”, salon “constructed sculpture”, da kuma salon zane na “Collage”,[1][2] da dai sauran salon zane da ya taimaka wajen bunkasawa. Daga cikin fitattun ayyukansa akwai Zanen Proto-Cubism, Zanen Les Demoiselles d'Avignon, da zanen anti-war da dai sauransu.

Picasso ya nuna bajinta da kwarewa a harkokin zane da dama a lokacin kuruciyarsa, inda yake zane acikin salo na musamman tun yana ƙarami har zuwa tsufansa. A farkon shekaru goma na karni na 20, salonsa sun canza yayinda ya ƙirƙiri kuma ya gwada sabbin dabaru da salo. Bayan shekarun 1906, dabarun tsohon mai zane Henri Matisse sun karawa Picasso karfin gwiwa sake nemo sabbin dabaru, wanda hakan ya janyo adawa a tsakanin masu zanen guda biyu, wadanda masu binciken zane suke alakantasu a matsayin jagororin masu zane na zamani.[3][4][5][6]

An rarraba ayyukan Pissaco zuwa lokuta daban daban. Yayinda har yanzu ana jayayya akan sunayen mafi akasarin ayyukansa. Lokutan ayyukansa da suka fi fice sune kamar haka: Lokacin Bula na Picasso (1901–1904), Lokacin Rose Picasso (1904–1906), Lokacin Zanen Afurkawa (1907–1909), Analytic Cubism (1909–1912), da kuma Synthetic Cubism (1912–1919) wanda kuma ake kira da Crystal Cubism. Mafi akasarin ayyukan Picasso a tsakanin shekarun 1910s da farkon shekarun 1920s sun kasance acikin salo irin na neoclassical sannan ayyukansa a tsakiyan shekarun 1920s suna da alaka da Surrealism. Ayyukansa na baya-baya suna da alaka da salonsa na tun yana karami.

Ya samar da zane da dama na musamman a daukakin rayuwarsa, Picasso ya samu shahara a duniya kuma ya tara dukiya mai yawa a dalilin nasarorinsa a zane kuma ya zamo daya daga cikin masu zane na musamman na ƙarni na 20.

Picasso with his sister Lola, 1889

An haifi Picasso da misalin karfe 23:15 na ranar 25 ga watan Oktoban shekara ta 1881, a birnin Malaga, Andalusiya, na Kudancin Sipaniya.[7] Ya kasance ɗa na fari ga mahaifinsa José Ruiz y Blasco (1838–1913) da mahaifiyarsa Picasso y López.[8] Iyayen Picasso sun kasance masu matsakaicin karfi. Mahaifinsa ya kasance mai zane wanda ya kware a zanen tsuntsaye da kuma wasanni. Mahaifinsa Ruiz ya kasance farfesa na fasaha a Makarantar Fikira kuma mai kula da wata tsohuwar gidan ajiyan kayan tarihi.[9] Kakannin Ruiz sun kasance kananun masu sarauta.

Shaidar haihuwar Picasso da baptizanshj na dauke da sunaye masu tsawo, wanda ya hada da malaman kirista da danginsa. Ruiz y Picasso sune sunayen kakanninsa na wurin uwa da na wurin uba bi da bi, dangane da al’adar mutanen Sipaniya. Sunan mahaifinsa “Picasso” ya samo asaline daga garin Liguria, wani yankin gabar teku da ke arewa-maso-yammacin Italy.[10] Kakan kakan pablo na wurin uwa Tommaso Picasso ya komo garin Sipaniya a shekarar 1807.[10]

Picasso ya fara samun horo daga wurin mahaifinsa a shekarar 1890. Ana iya samun tarin ayyukansa na farko-farko a gidan kayan tarihin Museu Picasso da ke Barcelona.[11] Ya zuwa shekara ta 1893, kwarewarsa na dan koyo ya fara karfi sannan ya zuwa shekara ta 1894 ya zama cikakken mai zane.[12] Ana iya ganin salon mmakarantar realism a zanensa na tsakiyar 1890s a zanensa na The First Communion (1896), wani babban zanen kanwansa mai suna Lola. Har ila yau, acikin wannan shekara ne yayi zanen Portrait of Aunt Pepa, wani zane na musamman dake ɗauke da fuskar Juan-Eduardo Cirlot, wana ake dauka a matsayin "daya daga cikin zanen da sukafi shahara a tarihin Sipaniya".[13]

Lokacin Bula 1901–1904

[gyara sashe | gyara masomin]
Picasso la vie.jpg

Lokacin ayyukan Picasso na Blue Period (1901–1904), lokaci ne na zanensa da ke da alaka da kalar bula da kuma bula-da-kore kadai, sai dai akan dan kara wasu kaloli a wasu lokutan, wanda ya soma ko dai a kasar Sipaniya a 1901 ko kuma a kasar Farisa a tsakiyar shekarar.[14] Mafiya yawancin zanunkansa na uwaye da 'ya'yansu wato gaunt mothers with children ya samo asali ne daga lokacin zanukansa na bula, a wannan lokacin ne rayuwar Picasso ta rabu a tsakanin kasar Barcelona da kuma Farisa. Acikin wani yanayi da yake amfani da kaloli a wajen nuna abu mara sha'awa - karuwa da masu bara ne muhimman al'amari. Ayyukan Picasso sun samo tushe daga tafiyarsa a cikin ƙasar Sipaniya da kuma kisan kan abokinsa Carles Casagemas. A farkon kakar 1901, yayi zanukan fuskar Casagema wanda ya samar da salon zane na La Vie (1903), yana nan yanzu a gidan tarihi na Cleveland Museum of Art.[15]

Wannan yanayi ne ya kara janyo habakar salon zanen The Frugal Repast (1904),[16] wanda ke nuna wani mutum makaho da kuma mata mai gani, wadanda gabaki dayansu sun galabaita, suna zaune a wani dan teburi. Makanta ya kasance muhimmin take a zanen Picasso na wannan lokaci, kamar acikin zanen The Blindman's Meal (1903, the Metropolitan Museum of Art) da kuma zanen fuskar Celestina (1903). Ayyukansa na wannan Lokaci na Bula sun hada da Zanen Fuskar Soler da kuma Zanen Fuskar Suzanne Bloch.

Lokacin Rose: 1904–1906

[gyara sashe | gyara masomin]

Lokacin Rose (1904–1906)[17] na da alaka da kalar fata mai haske ta hanyar amfani da kalar lemu da kalar pink wanda ya kunshi 'yan wasa da dai sauransu.

Lokacin Zanen Afurkawa: 1907–1909

[gyara sashe | gyara masomin]
Les Demoiselles d'Avignon.jpg

Lokacin zanen Picasso da ya samu tasiri daga mutanen Afurka (1907–1909) ya fara ne da zanensa na farko na Les Demoiselles d'Avignon.

Analytic cubism: 1909–1912

[gyara sashe | gyara masomin]

Ccubism (1909–1912) wani salo ne na zane da Picasso ya ƙirƙira tare da [Georges Braque]] hanyar amfani da launin ruwan kasa mai duhu da sauran kaloli daban daban. Wadannan masu zane guda biyu suna daukan abubuwa su zana su dangane da ainihin sifarsu. Zanen Picasso da na Braque na wannan lokacin suna da kamiceceniya sosai.

Synthetic cubism: 1912–1919

[gyara sashe | gyara masomin]
Picasso in front of his painting The Aficionado (Kunstmuseum Basel) at Villa les Clochettes, summer 1912

Synthetic cubism (1912–1919) cigaba ne a salon zane na cubism, inda ake jera yankakken takarda mafi yawanci bangon littafi ko kuma wani shashe na jarida - ana jera su don bada wata sifa, wanda ya janyo mafarin salon zanen collage a kimiyar zane.

Pablo Picasso

A tsakanin 1915 zuwa 1917, Picasso ya fara wani sabon salon zane wanda ke nuna abubuwa daban daban, wanda ya kunshi jita, ko gilashi, da wani kamaiceceniya irinta collage.

  1. “The Guitar, MoMA". Moma.org. Retrieved 3 February2012.
  2. "Sculpture, Tate". Tate.org.uk. Archived from the originalon 3 February 2012. Retrieved 3 February 2012.
  3. "Matisse Picasso – Exhibition at Tate Modern". Tate.
  4. Green, Christopher (2003), Art in France: 1900–1940, New Haven, Conn: Yale University Press, p. 77, ISBN 0-300-09908-8, retrieved 10 February 2013
  5. Searle, Adrian (7 May 2002). "A momentous, tremendous exhibition". The Guardian. UK. Retrieved 13 February 2010.
  6. "Matisse and Picasso Paul Trachtman, Smithsonian, February 2003" (PDF).
  7. Cabanne, Pierre (1977). Pablo Picasso: His Life and Times. Morrow. p. 15. ISBN 978-0-688-03232-6.
  8. Hamilton, George H. (1976). "Picasso, Pablo Ruiz Y". In William D. Halsey (ed.). Collier's Encyclopedia. Vol. 19. New York: Macmillan Educational Corporation. pp. 25–26.
  9. Daix, Pierre (1988). Picasso, 1900–1906: catalogue raisonné de l'oeuvre peint (in French). Editions Ides et Calendes. pp. 1–106.
  10. 10.0 10.1 Antepasados y familiares de Picasso, Fundación Picasso, Museo Casa Natal, Ayuntamiento de Málaga"(PDF
  11. Cirlot 1972, p. 6.
  12. Cirlot 1972, p. 14.
  13. Cirlot 1972, p. 37.
  14. Cirlot 1972, p. 127.
  15. Wattenmaker, Distel, et al. 1993, p. 304.
  16. The Frugal Repast, Metropolitan Museum of Art. Retrieved 11 March 2010.
  17. Wattenmaker, Distel, et al. 1993, p. 194.