Barcelona

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Barcelona.

Barcelona (lafazi: /bareselona/) birni ce, da ke a yankin Katalunya, a ƙasar Hispania. Ita ce babban birnin yankin Katalunya. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2015, akwai jimilar mutane 5,375,774 (miliyan biyar da dubu dari uku da saba'in da biyar da dari bakwai da saba'in da huɗu). An gina birnin Barcelona kafin karni na ɗaya kafin haifuwan annabi Issa.