Mustapha Musty
Mustapha Musty Tsohon jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato masana'antar Kannywood, fitaccen jarumi Kuma sannanne a masana'antar fim ta Hausa. Yayi fina finai da dama a masana'antar fim ta Hausa[1]
Takaitaccen Tarihin sa
[gyara sashe | gyara masomin]Mustapha musty an haifeshi ne a Jihar Kano Karamar hukumar a kwataz din gyadi gyadi, suna mustapha mustapha anfi Kiran sa da mustapha musty, yayi karatun firamare a gyadi gyadi firamare school, yayi karatun sakandiri a kofar sabuwar sakandiri school kusa da Jami'ar BUk, gefen kwalejin Rumfa, daga Nan ya tafi makarantar gwamnati Mai suna foliteknik kwalej, daga nan kuma ya shiga jami'ar Bayero university Kano yayi diploma inda ya Karanci public administration, bayan Nan yayi aiki a kamfanin kakansa (Ila enterprises limited)bayan Nan ya shiga harkan fim, ta hanyar abokan sa inda kuma wasu furodusa ne wasu daraktas wasu kuma jarumai,fim din farko da ya fara sunan shi (Hawainiya)Wanda margayi furodusa[2] hamza Danzaki yai furodusin, Musty yayi aure inda ya auri Soha bayan sun shafe shekaru 13 suna soyayyah, cikaken sunan ta ghadir muhamud sharif, an daura auren a ranar lahadi 29 satumba a shekarar 2020.[3]bayan wata goma dayin auren su suka haifi yaro namiji.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://hausamini.com.ng/video-musty-fashion-bani-dama-official-video/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.
- ↑ http://hausafilms.tv/actor/mustapha_musty
- ↑ https://fimmagazine.com/bayan-wata-10-mustapha-musty-da-soha-sun-samu-%C9%97an-fari/