Musulunci a Rasha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Musulunci a Rasha
Classification

Musulunci shine addini na biyu mafi girma a Rasha, bayan Kiristanci na Orthodox . An kuma ce addinin Musulunci shi ne addini mafi saurin bunƙasa a ƙasar kuma yana ɗaukar sama da 7% na yawan mutanen Rasha zuwa kashi daya bisa biyar na yawan mutanen, da kashi 24%. Yana da yawa a cikin ƙabilun Rasha, kuma yawancinsu musulmai ne na Sunni na mazhabar Hanafiyya.