Nakatindi Wina

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nakatindi Wina
Member of the National Assembly of Zambia (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Zambiya, 15 ga Faburairu, 1945
ƙasa Zambiya
Mutuwa Johannesburg, 5 ga Afirilu, 2012
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Movement for Multi-Party Democracy (en) Fassara

Gimbiya Naganda Nakatindi Wina (15 Fabrairu 1945 - 5 Afrilu 2012) [1] yar siyasar Zambia ce kuma memba ce a cikin gidan sarauta na Barotseland.

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Gimbiya Naganda Nakatindi Wina Mukwae Nakatindi a cikin gidan sarautar Barotseland, jikanyar Sarki Yeta III na mutanen Lozi, Nakatindi 'yar Nakatindi Yeta Nganga ce da Induna Yuyi Nganda; ɗaya daga cikin yara 11.[ana buƙatar hujja]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan gabatar da siyasar jam’iyyu da yawa a farkon shekarun 1990, ta shiga jam’iyyar Movement for Multi-Party Democracy kuma a 1992 ta zama minista da kanta lokacin da aka naɗa ta a matsayin karamar ministar yawon bude ido. A shekara ta 1994 ta zama ministar ci gaban al'umma da walwalar jama'a.

Rigingimu[gyara sashe | gyara masomin]

A farkon shekarun 1990, an yi ƙwarya-kwaryar jerin badakalar shigo da kwayoyi masu alaƙa da 'yan siyasar na jam'iyyar MMD. Steve Denning na Bankin Duniya ya ba da shawarar ga Frederick Chiluba, Shugaban Zambiya, ya magance lamarin. Nakatindi Wina, dai na da alaƙa da badakalar da jaridun ƙasar Zambia suka yi, amma Chiluba ya ki ya kore ta. A maimakon haka, ya zargi ƙafafen yaɗa labarai da yin ƙarin gishiri a lamarin.[2] Duk da haka, daga baya ya ɗaure ta a gidan yari a 1998,[3] bayan da aka danganta ta da yunkurin juyin mulkin 1997 na Zambia. An tsare ta a Gidan yarin Mukobeko, inda mijinta, Induna Sikota Wina, ya zauna da ita. Ya zargi ɗan siyasa Michael Sata da yi wa Chiluba karya don ya nuna zargi ga Nakatindi Wina.[4]

A shekara ta 2000, ta yi kira ga mata da su ƙauracewa Tarayyar Afirka saboda rashin daidaiton jinsi a cikin wakilan; kamar yadda aka buƙaci kowace ƙasa ta sanya mace ɗaya a matsayin mafi ƙarancin a cikin kungiyoyin wakilan. Ta ce shugabannin maza suna son mata ne kawai su zama "furanni masu launi" a cikin ƙungiyar.[5]

Rashin lafiya da mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin 2012, an gano cewa tana da ciwon zuciya kuma an kai ta asibiti a Johannesburg, Afirka ta Kudu. Ta rasu bayan tiyatar da aka yi mata a ranar 5 ga Afrilun 2012. Daga baya ɗanta, Wina Wina, ya gode wa hukumomin Afirka ta Kudu da suka ba ta magani a can.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Sata leads scores of mourners to pay repects to Princess Nakatindi QFM, 13 April 2012
  2. Ihonvbere, Julius O. (November 1993). "Threats to Democratization in Sub-Saharan Africa: The Case of Zambia". Journal of Asian and African Studies. 27 (3): 229.
  3. "HRW World Report 1999: Zambia: Human Rights Developments". www.hrw.org. Retrieved 2022-05-24.
  4. "Sata should know this, declarations are not development". Zambian Watchdog. 27 November 2012. Retrieved 4 November 2017.
  5. Akyeampong, Emmanuel Kwaku; Gates, Jr., Henry Louis (2012). Dictionary of African Biography. New York: Oxford University Press. pp. 164–165. ISBN 978-0-195382-075.
  6. "Princess Nakatindi Wina has died". Lusaka Times. 6 April 2012. Retrieved 4 November 2017.