Ndudi Elumelu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ndudi Elumelu
minority leader (en) Fassara

ga Yuli, 2019 -
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 -
Rayuwa
Haihuwa 23 ga Faburairu, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Ahali Tony Elumelu
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Ndudi Godwin Elumelu (an haife shi ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 1965) ɗan siyasar Najeriya ne mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Aniocha da Oshimili a majalisar wakilai,[1] A halin yanzu shine shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai.[2] kuma ƙane ga Tony Elumelu.

Bayanan baya da farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ndudi ya samu shaidar kammala karatunsa na Sakandare na yammacin Afirka daga makarantar fasaha da kimiyya ta jihar Legas a shekarar 1986, sannan ya samu Diploma ta a ƙasa kan harkokin kasuwanci a Kwalejin Fasaha ta Yaba a shekarar 1989. A cikin shekarar 1993, ya sami digiri a fannin lissafin kuɗi daga Jami’ar Jihar Edo, Ekpoma, sannan ya yi digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci a wannan makaranta a shekarar 2000.[3]

Sana'ar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An fara zaɓen Ndudi a matsayin ɗan majalisar wakilai a shekarar 2007 kuma an sake zaɓen shi a shekarar 2011.[4] A wa'adinsa na farko na biyu, ya kasance shugaban kwamitin kula da wutar lantarki daga shekarar 2007 zuwa 2010 da kuma shugaban kwamitin kula da lafiya na majalisar daga shekarar 2011 zuwa 2015.[1] A shekara ta 2014, ya tsaya takarar gwamnan jihar Delta wanda ya sha kaye,[5][6] ta haka ya rasa kujerarsa a gidan a hannun Joan Onyemaechi Mrakpor.[7] A shekarar 2019, ya sake komawa majalisar wakilai karo na uku.[8][9][10]

A shekarar 2021, Mista Ndudi Elumelu ya ƙaddamar da shirin ƙarfafawa mutane 456 da aka zaɓa daga Mazaɓar.[11] A shekarar 2022, ya lashe zaɓen fidda gwani na majalisar wakilai ta jam'iyyar People's Democratic Party.[12][13][14] A cikin watan Fabrairun 2023, ya sha kaye a zaɓen majalisar wakilai a hannun ƴar takarar jam'iyyar Labour Ngozi Okolie.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 https://nass.gov.ng/mps/single/10
  2. https://www.vanguardngr.com/2021/05/house-of-reps-minority-leader-elumelu-empowers-456-constituents/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-04-01. Retrieved 2023-04-01.
  4. https://www.vanguardngr.com/2022/06/elumelu-yet-another-opportunity/
  5. https://www.vanguardngr.com/2014/12/pdp-governorship-primaries-ribadu-folarin-okowa-agbaje-others-win/
  6. https://saharareporters.com/2014/12/08/uduaghan-disgraced-okowa-wins-delta-pdp-gov-primary
  7. https://guardian.ng/politics/mrakpor-women-wont-get-power-without-fighting-for-it/
  8. https://www.channelstv.com/2019/02/25/senator-nwaoboshi-elumelu-win-nass-elections/
  9. https://www.vanguardngr.com/2019/02/elumelu-of-pdp-wins-aniocha-oshimili-fed-constituency-in-delta/
  10. https://guardian.ng/news/elumelu-declared-winner-of-house-of-reps-election-in-delta/
  11. https://guardian.ng/news/elumelu-supports-constituents-with-n300m-worth-of-machines/
  12. https://www.channelstv.com/2022/05/22/pdp-reps-primaries-elumelu-emerges-as-candidate-for-aniocha-oshimili-constituency/amp/
  13. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-07-06. Retrieved 2023-04-01.
  14. https://www.premiumtimesng.com/news/more-news/531679-elumelu-wins-pdp-primaries.html