Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare a Yammacin Afurka (WASSCE)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare a Yammacin Afurka (WASSCE)
kwaji da secondary school leaving qualification (en) Fassara
Bayanai
Bangare na National Curriculum of Ghana (en) Fassara
Ƙasa Ghana da Najeriya
Ma'aikaci West African Examinations Council (en) Fassara

Jarrabawar Manyan Makarantun Sakandare na Yammacin Afirka ( WASSCE ) nau'in jarabawa ce ta tantancewa a Yammacin Afirka. Daliban da suka ci jarrabawar sukan samu takardar shaidar kammala karatunsu na sakandare,Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ce ke gudanar da jarabawar,[1] Ana ba da ita kawai ga daliban da ke zaune a ƙasashen yammacin Afirka ta Anglophone. Ana kiran takardun shaidar kammala karatun sakandare da ake bayar wa bayan nasarar kammala jarrabawar West African Senior School Certificate (WASSCE).

Jarabawar ta WASSCE ta kunshi gwaji akan mahimman darussa guda huɗu - Turanci, lissafi, kimiyya, nazarin zamantakewa, da sauran zababbun darussa guda uku ko huɗu.[2]

Jarabawowin[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai nau'ikan jarrabawar WASSCE iri biyu:

  • WASSCE don 'Yan Makaranta (Mayu/Yuni) ita ce Jarrabawar Takaddar kammala manyan azuzuwa na sakandare (SSCE) ga daliaban makaranta. Daliban shekarar karshe a manyan azuzuwan makarantun sakandare ne ke daukar jarabawar. Suna sanya kayan makarantun su daban-daban. Ana ba da wannan jarrabawar a lokacin bazara (Afrilu zuwa Mayu), kuma sakamakon kan fito a watan Agusta.
  • WASSCE na dalibai masu zaman kansu (Jan/Feb da Nov/Dec), wanda kuma aka fi sani da General Certificate Examination (GCE) ko WAEC GCE, jarrabawa ce ta sirri kuma ba a buƙatar yunifom, amma rajista na shatar hannu ya zama dole kamar yadda ake yi a da. Ana yin wannan jarrabawar ne a farkon bazara (wanda aka fi sani da silsilar farko ) ko kuma kaka (wanda aka sani da silsilar ta biyu ), kuma yawanci waɗanda suka kammala karatun sakandare ne waɗanda suke son gyara kurakuran sakamakonsu. Ana samun sakamakon nan da Maris ko Disamba, yawanci kwanaki 45 bayan rubuta takarda ta ƙarshe.

A karkashin tsarin bada maki na WAEC, ana amfani da haruffa A zuwa F don nuna kyakkyawan sakamako (yayin da lambobi 1-9 ana amfani da su ne kawai don tantance maki). A takaice, don samun A1 a cikin darasi, jarabawar WASSCE a lissafi misali, kuna buƙatar maki aƙalla 75%. Yin haka yana nufin za ku iya samun tambayoyi 75 daidai cikin 100.

A ƙasa akwai bayanai kan tsarin tantancewa, da kuma maki da jami'o'in Najeriya ke amfani da su wajen tantance ɗaliban da za su kammala karatun digiri na farko a shekarar 2021.

Daraja Daidaiton Lambobi (%) Maki (%) Magana
A1 75-100 8 Madalla
B2 70-74 7 Yayi kyau sosai
B3 65-69 6 Yayi kyau
C4 60-64 5 Kiredit
C5 55-59 4 Kiredit
C6 50-54 3 Kiredit
D7 45-49 0 Wuce
E8 40-44 0 Wuce
F9 0-39 0 Kasa

Ana iya fahimta daga wannan teburi cewa mafi ƙarancin ƙimar wucewa shine C6 (ba tare da la'akari da yabo ba). Ana shawartar dalibai da ke da D7 zuwa ƙasa (musamman a Lissafi da Turanshi) da su sake yin jarrabawar idan suna son ci gaba da karatun manyan makarantu da ake samun ilimin digiri.

Dokokin Shiga Jami'a[gyara sashe | gyara masomin]

Ana shawartar dalibai da cewa za a bukaci su da su cika sharuddan da kowacce jami’a ke buƙata har ma da buƙatun fannukan darasi daban daban na jami’ar da suke son shiga kuma waɗannan buƙatun sun bambanta sosai. Ana iya samun takamaiman bayanai na shiga da ƙa'idodin kora daga jami'o'i ko ƙungiyoyin ƙwararrun wanda abin ya shafa.

Najeriya[gyara sashe | gyara masomin]

Daliban manyan makarantun Sakandare na Najeriya na iya yin jarrabawar WASSCE ko jarabawar National Examination Council (NECO).

Daliban da suka zabi yin karatu a jami’o’in Najeriya, ana bukatar su rubuta jarabawar shiga jami’o’i (Uniified Tertiary Matriculation Examination (UTME)’ wato jarrabawar shiga jami’o’in da hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ke gudanarwa.

Ƙasar Ingila[gyara sashe | gyara masomin]

Jami'o'in da ke turai wato United Kingdom na iya bukata daga dalibai ƙarin takardar kammala kwas na tushe na shekara ɗaya ko makamancin hakan. Tabbacin ƙwarewa a Turanci na iya zama wajibi.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Karen Wells (8 November 2019). Teen Lives around the World: A Global Encyclopedia [2 volumes]. ABC-CLIO. p. 330. ISBN 978-1-4408-5245-9.
  2. "Coert Loock; Vanessa Scherman (20 November 2019). Educational Assessment in a Time of Reform: Standards and Standard Setting for Excellence in Education. Taylor & Francis. p. 27. ISBN 978-0-429-68547-7.
  3. "Guidelines for university entrance". West African Examination Council, Nigeria portal – via waecnigeria.org.