Niki Tobi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Niki Tobi
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Niki (en) Fassara
Sunan dangi Tobi
Shekarun haihuwa 14 ga Yuli, 1940
Wurin haihuwa Delta
Lokacin mutuwa 19 ga Yuni, 2016
Sana'a mai shari'a
Ilimi a Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya

Niki Tobi, CON (ranar 14 ga watan Yulin 1940 - ranar 19 ga watan Yuin 2016) ya kasance mataimakin alƙalin kotun ƙolin Najeriya. An haifi Tobi ne a garin Esanma dake ƙaramar hukumar Bomadi a jihar Delta a yanzu. Kafin ya fara aiki a benci, ya kasance shugaban tsangayar shari’a kuma mataimakin shugaban jami’ar Maiduguri (academic services). An naɗa shi Kotun Ƙoli a shekarar 2002.[1]

An san shi da ƙwararren shari'a da kuma sanin ƙa'idodin shari'a. Ya rasu a ranar 19 ga watan Yunin 2016.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://web.archive.org/web/20070908215435/http://www.scn.gov.ng/portal/detail.php?link=niki
  2. https://ynaija.com/supreme-court-justice-dead-niki-tobi/