Olivier Boissy

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Olivier Boissy
Rayuwa
Haihuwa Dakar, 1999 (24/25 shekaru)
ƙasa Faransa
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Olivier Stephane Boissy (an haife shi a cikin shekara ta 1999) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ta ƙasar Senegal wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Faransa Saint-Pryvé a matsayin aro daga Grenoble.[1]

Aikin kulob[gyara sashe | gyara masomin]

Boissy ya fara babban aikinsa a Ghana tare da Accra Lions, kafin ya shiga ɓangaren ajiyar Hapoel Petah Tikva a cikin shekarar 2017, kafin ya sake komawa Accra Lions a cikin shekarar 2018.[2] Daga nan ya koma Salitas da ke Burkina Faso, inda ya zura ƙwallaye 21 a dukkan gasa a kakarsa ta farko.[3] A ranar 17 ga watan Yulin 2021, ya koma Grenoble a gasar Ligue 2 ta Faransa.[4] Ya fara wasansa na ƙwararru tare da Grenoble a cikin rashin nasara da ci 4-0 a gasar Ligue 2 a hannun Paris FC a ranar 24 ga watan Yulin 2021.[5]

A ranar 1 ga watan Fabrairun 2023, an bada Boissy aro ga Saint-Pryvé a Championnat National 2.[6]

Ayyukan ƙasa da ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

Boissy matashi ne na ƙasa da ƙasa na Senegal, wanda ya wakilci Senegal U20s sau daya a cikin shekarar 2017.refe[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]