Oluwole Oke
Oluwole Oke | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Obokun/Oriade
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 28 ga Afirilu, 1967 (57 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Abuja Jami'ar Obafemi Awolowo University of London (en) | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan kasuwa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | People's Democracy Party (en) |
Oluwole Busayo Oke (an haife shi ranar 28 ga watan Afrilu 1967) ɗan kasuwan Najeriya ne, mai gudanarwa, masanin tattalin arziki kuma ɗan siyasa wanda ke aiki a Majalisar Wakilai ta 8 kuma ta yanzu.[1] Shi ne shugaban kwamitin asusun gwamnati a majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar mazabar Obokun/Oriade na jihar Osun a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party a Najeriya.[2][3]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Oluwole Oke ya halarci kwalejin kimiyya da fasaha ta Ibadan, inda ya samu shaidar karatunsa na kasa a shekarar 1988 a fannin kasuwanci. Daga nan ya wuce Jami’ar Abuja inda ya sami digiri na farko a fannin tattalin arziki a shekarar 1999. Ya kuma yi karatun MBA daga fitaccen jami’ar Obafemi Awolowo University ile ife a shekarar 2004 A shekarar 2013, ya halarci Jami’ar Landan inda ya sami digiri na biyu.[4][5]
Aikin majalisa
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1999, an zabi Oke a majalisar wakilai ta Najeriya mai wakiltar mazabar Oriade / Obokun na jihar Osun. Oke ya yi aiki a matsayin memba kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar a tsakanin 2003 zuwa 2011. Ya yi rashin nasarar komawa kan kujerarsa a 2011, daga baya kuma ya sake tsayawa takara a 2015 kuma ya yi nasara. Bukatunsa na doka sun haɗa da ilimi, haraji, mai da iskar gas da sayayya.[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Assembly, Nigerian National. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". www.nass.gov.ng. Retrieved 19 March 2018.
- ↑ Nigeria Legislature 1861–2011: A Compendium of Members & Officials : a Special Publication in Commemoration of Nigeria at 50 (in Turanci). Department of Information and Publications, National Assembly. 1 January 2010. ISBN 9789789113262.
- ↑ "Reps give FMBN ex-boss 48 hours to render account". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-03-10. Archived from the original on 2022-02-21. Retrieved 2022-02-21.
- ↑ Admin. "Hon Busayo Oluwole Oke". Osun govt. Archived from the original on 20 March 2018. Retrieved 19 March 2018.
- ↑ Admin. "Oluwole Oke". OluwoleOke. Archived from the original on 18 January 2018. Retrieved 19 March 2018.
- ↑ Admin. "Oke Busayo". Blerf. Retrieved 19 March 2018.