Jump to content

Oriyomi Hamzat

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Oriyomi Hamzat
Oriyomi Hamzat
Haihuwa Oriyomi Abdulrahman Hamzat
Ibadan, Oyo State, Nigeria
Aiki

Journalist

human rights activist
Iyaye(s) Asimiyu Adekunle Hamzat, (father)
Lamban girma

Honorary Doctorate in Art and Communications.

International Humanitarian Service Award.

Oriyomi Abdulrahman Hamzat 'Dan jaridar watsa shirye-shirye ne a kasar Najeriya kuma mai fafutukar kare hakkin bil'adama wanda ya ke aiki a matsayin Shugaban Agidigbo 88.7 FM . [1][2]

Tarihi da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Hamzat ne a garin Ibadan, jihar Oyo, a kasar Najeriya, inda kuma anan ya girma, ga mahaifinsa Asimiyu Adekunle Hamzat, wadda shima ɗan jarida ne na Hukumar Talabijin ta Najeriya wato NTA. Hamzat ya samu ya kammala karatunsa na makarantar sakandare ne a makarantar Iroko Community Grammar School kafin ya ci gaba zuwa Makarantar Kimiyya ta Jihar Oyo, Pade . Ya sami difloma a fannin ilimin ƙasa daga The Polytechnic, Ibadan, kuma ya ci gaba da karatu kan Sadarwar Jama'a a Cibiyar Eruwa (wanda yanzu ake kira Adeseun Ogundoyin Polytechnic. A watan Nuwamba na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku (2023), Hamzat ya sami digiri na farko a fannin ilimin harshe da harshe daga Jami'ar Ibadan . [3]

Hamzat ya fara aiki ne a matsayin ɗan jarida mai buga takardu na jaridar Najeriya mai suna The Guardian . Bayannan kuma ya yi aiki a kungiyoyi masu yawa ciki har da Kamfanin Watsa Labarai ta Jihar Oyo wato (BCOS) wadda take Ile Akede, Ibadan, Kamfanin Rediyo na Tarayya na Najeriya, Raypower, da 32 FM 94.9. Bayan kwarewarsa ta aiki a cikin kafofin watsa labarai, ya ƙaddamar da nasa dandamali mai suna Agidigbo 88.7 FM . [4]

Ɗaya daga cikin sanannun gudummawarsa shine ba da ra'ayi gameda 'yan Najeriya da aka ware gefe guda da kuma wadda basuda muryar gaya a ji.[5][6] A game da Timothy Adegoke, wani dalibi wanda mutuwarsa a karkashin yanayi mai ban mamaki ya haifar da fushi Hamzat ya shiga tsakani.[7][8][9][10]

A cikin shekarar dubu biyu da sha bakwai (2017), Ma'aikatar Tsaro ta Jiha ta kama shi kan tuhumar ƙarya.[11][12]

Kyaututtuka da karbuwa

[gyara sashe | gyara masomin]
Kyautar Bayani Ranar Tabbacin.
Dokta na girmamawa a cikin Fasaha da Sadarwa. Jami'ar Turai-Amurka ce ta bayar da shi a matsayin D.Art, Honoris Causa . Afrilu 2023. [13]
Kyautar Ayyukan Jama'a ta Duniya. An karɓa don gudummawa mai ban mamaki ga aikin jin kai. Satumba 2023. [14][15]

Gidauniyar Taimako ta Oriyomi Hamzat

[gyara sashe | gyara masomin]

Oriyomi Hamzat kuma yana da gidauniyar sadaka inda yake kula da yara marasa uwa ko kuma marayu, yana ɗaukar nauyin ciyarwa da tallafawa iliminsu.

Oriyomi Hamzat gifting his staff a car
Oriyomi Hamzat ya ba ma'aikatansa mota

Kwanan nan ba da jimawa ba ya ba da kyautar motoci ga ma'aikatansa waɗanda suka yi aiki tare da shi a tsohon gidan rediyon sa na Agidigbo 88.7 FM

  1. Kabiru, Toheeb (12 June 2024). "Oriyomi Hamzat Biography, Net Worth, Age, Wife, Daughter, Cars, Houses, Radio Stations And Lifestyle Full Version". Talk49ja. Retrieved May 6, 2024.
  2. "Why investigative journalism is difficult in broadcast industry — Agidigbo FM manager". Premium Times. 4 May 2021.
  3. "Agidigbo FM Chairman, Oriyomi Hamzat, One Other Bag Bachelor's Degree From UI". Independent Newspaper. 15 November 2023.
  4. "Makinde pledges to support Agidigbo FM". PM News Nigeria. 26 March 2021.
  5. "Man in tears after DNA test reveals he's not biological father of his four children". Nigerian Tribune. 5 November 2023.
  6. "I found myself under Oshodi bridge after 21 years in the US — a Nigerian man". Vanguard News. 20 November 2023.
  7. "Timothy Adegoke: Stop intimidating Oyo broadcaster, lawyer warns police". Punch Newspaper. 24 May 2023.
  8. "FIB Arrests Radio Presenter Oriyomi Hamzat 'Over Comments on Timothy Adegoke's Murder'". Foundation for Investigative Journalism. 26 May 2022.
  9. "Alleged killing of Timothy: Ibadan-based Radio CEO, Hamzat regains freedom". Vanguard Newspaper. 27 May 2022.
  10. "Timothy Adegoke: Arrest, intimidation of Hamzat is illegal, unconstitutional – Lawyer warns IGP". Daily Post Nigeria. 23 May 2023.
  11. "Broadcaster accused of murder granted N2m bail". The Nation Newspaper. 22 August 2017.
  12. "Court strikes out murder case against Agidigbo FM proprietor, 4 others". The Guardian. 10 January 2023.
  13. "Oriyomi Hamzat Bags Honorary Doctorate in Arts from European-American University". Inside Oyo News. 29 April 2023.
  14. "Dr. Oriyomi Hamzat Chairman of Agidigbo FM Receives International Humanitarian Award". Primus Media city. 9 September 2023.
  15. "Agidigbo FM Boss, Oriyomi Hamzat, Receives Award For His Humanitarian Service". Inside Oyo News. 9 September 2023.