Ouhoumoudou Mahamadou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ouhoumoudou Mahamadou
firaministan Jamhuriyar Nijar

3 ga Afirilu, 2021 - 26 ga Yuli, 2023
Brigi Rafini
Minister of Finance of Niger (en) Fassara

21 ga Afirilu, 2011 - 2 ga Afirilu, 2012 - Gilles Baillet (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Amaloul Nomade (en) Fassara, 1954 (69/70 shekaru)
ƙasa Nijar
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Nigerien Party for Democracy and Socialism

Ouhoumoudou Mahamadou shekarar (1954-) ɗan siyasan Nijar ne na Jam’iyyar Demokraɗiyya da Gurguzu ta Jamhuriyar Nijar wato (PNDS-Tarayya) wanda kuma yake aiki a matsayin Firayim Ministan Nijar tun daga ranar 3 ga watan Afrilu shekarar 2021 .

Ouhoumoudou Mahamadou

Mahamadou ya yi aiki a gwamnatin Nijar a matsayin Ministan Ma'adinai, Makamashi, da Masana'antu daga shekarar 1991 zuwa shekara ta 1993 da kuma Ministan Kuɗi daga watan Afrilun shekarar 2011 zuwa watan Afrilun shekarar 2012. Ya kasance Darakta a majalisar zartarwar shugaban ƙasa tun daga shekarar 2015.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin gwamnatin riƙon ƙwarya ta Firayim Minista Ahmadou Cheiffou, wanda aka naɗa a ranar 7 ga watan Nuwamban shekarar 1991, Mahamadou ya kasance Ministan Ma'adanai, Makamashi, Masana'antu, da ƙere-ƙere. [1] An ci gaba da rike shi a mukaminsa a cikin garambawul a majalisar zartarwa a ranar 31 ga Janairun 1993. [2] An gudanar da zabubbuka masu yawa a watan Fabrairun shekarar 1993, wanda ya kawo karshen mika mulki; Ba a saka Mahamadou cikin gwamnatin da aka nada a ranar 23 ga watan Afrilu shekarar 1993. [3] Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) a karkashin jagorancin Babban Sakatare Édouard Benjamin daga shekarar 1993 har zuwa shekara ta 1998 [4] sannan ya yi aiki a matsayin Wakilin Yankin Taimakon Lutheran na Yankin Afirka ta Yamma. [5]

Bayan da shugaban PNDS Mahamadou Issoufou ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairu da watan Maris shekarar 2011 kuma ya hau karagar mulki a matsayin shugaban ƙasar Nijer, an nada Ouhoumoudou Mahamadou a cikin gwamnatin a matsayin Ministan Kudi a ranar 21 ga watan Afrilu shekarar 2011. [6]

Mahamadou ya yi aiki a matsayin Ministan Kuɗi na ƙasa da shekara guda; an kore shi daga gwamnati a ranar 2 ga watan Afrilu shekarar 2012. [7] Daga baya a cikin wannan watan, an nada shi a matsayin Babban Darakta na Banque Internationale pour l'Afrique au Niger (BIA-Niger), babban banki. [8]

Ouhoumoudou Mahamadou

An naɗa Mahamadou a matsayin Darakta a majalisar zartarwa ta Shugaban kasa a ranar 4 ga watan Yunin shekara ta 2015. [9] Bayan an rantsar da Issoufou a wa’adi na biyu, ya ci gaba da rike Mahamadou a matsayinsa na Darakta a majalisar zartarwar shugaban kasar a ranar 11 ga watan Afrilu shekarar 2016. [10] [11]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Africa Research Bulletin: Political Series, volumes 28–29 (1991), page 10,336.
  2. Marchés tropicaux et méditerranéens, issues 2,460–2,485 (1993), page 356 (in French).
  3. Bulletin de l'Afrique noire, issues 1,615–1,659 (1993), page 202 (in French).
  4. The Weekly Review (1996), page 25.
  5. "Q&A with Mahamadou Ouhoumoudou" Archived 2010-12-19 at the Wayback Machine, Lutheran World Relief, 19 February 2009.
  6. "Niger unveils new government", Agence France-Presse, 21 April 2011.
  7. Aboubacar Yacouba Barma, "Les raisons d’un si léger remaniement" Archived 2013-06-24 at Archive.today, ActuNiger, 2 April 2012 (in French).
  8. Aboubacar Yacouba Barma, "Ouhoumoudou Mahamadou recyclé à la tête de la BIA"[permanent dead link], ActuNiger, 30 April 2012 (in French).
  9. Aboubacar Yacouba Barma, "Remaniement technique du gouvernement : Jeu de chaises musicales au PNDS", ActuNiger, 4 June 2015 (in French).
  10. "Composition du gouvernement de la République du Niger : La Renaissance « acte 2 » en marche", ActuNiger, 11 April 2016 (in French).
  11. Boureima Balima (April 4, 2021), Niger's President Bazoum appoints former minister Mahamadou as PM Reuters.