Jump to content

Patrick Aga

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Patrick Aga
mutum
Bayanai
Bangare na Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) Fassara
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Patrick
Wurin haihuwa Nasarawa
Harsuna Faransanci
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mayor of Mont-la-Ville (en) Fassara
Wurin aiki Mont-la-Ville (en) Fassara
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party da Alliance for Democracy (en) Fassara
aga

Patrick Aga an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Arewa a jihar Nasarawa dake Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu a Najeriya, inda ya tsaya takara a jam'iyyar PDP. Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999.[1] Bayan ya hau kan kujerar majalisar dattawa a cikin watan Yunin shekarar 1999, an naɗa shi a kwamitocin ɗa’a, shari’a, harkokin mata, kasuwanci, ilimi, ayyuka na musamman da basukan gida da waje (mataimakin shugaba).[2]

Patrick Aga

Ana gab da zaɓen shekarar 2003 Aga ya koma jam’iyyar Alliance for Democracy (AD) da fatan a zaɓe shi matsayin gwamnan Nasarawa a wannan dandali.[3] Bayan zaɓen jam'iyyar AD ta rabu gida biyu masu adawa da juna. A cikin watan Disamban shekarar 2003 aka naɗa Aga mataimakin shugaban yankin Arewa ta tsakiya na ƙasa a ƙarƙashin jagorancin Cif Adebisi Akande.[4]