Penda Mbow

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Penda Mbow
Rayuwa
Haihuwa Dakar, 4 ga Janairu, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Senegal
Ƴan uwa
Abokiyar zama Saliou Mbaye (en) Fassara  (2017 -
Karatu
Thesis director Charles-Marie de La Roncière (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Masanin tarihi da Mai kare hakkin mata
Employers Université Cheikh Anta Diop (en) Fassara

Penda Mbow, an haife ta shekaran 1955, yar tarihi ce, 'yar gwagwarmaya, kuma 'yar siyasan Senegal. Ministar Al'adun Senegal ta tsawon watanni da yawa a cikin shekaran 2001, farfesa ce a Jami'ar Cheikh Anta Diop a Dakar kuma shugabar motsawa ce yar kasa (yar kasa Mai tafiye tafiye).

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Penda Mbow a watan Afrilun shekaran 1955.

A cikin shekaran 1986 ta sami digiri na uku a tarihin Medieval a Université de Provence a Faransa, tare da kasida mai taken L'aristocratie militaire mameluke d'après le cadastre d'Ibn al-Ji'an : éléments de comparaison avec la France (a Turanci: The Mameluke Military Aristocracy bayan Jama'a Rajista na Ibn al-Ji'an: Elements of Comparison with France). Binciken karatunta ya mayar da hankali kan tarihin basirar Afirka da nazarin jinsi na Musulunci. Ya zama farfesa a shekara ta 2010.

Lambobin yabo da Karramawa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Tallafin karatu na Fulbright, jami'ar jihar Michigan
  • Lambar yabo na Rockefeller Foundation, akan bincike a cibiyar Bellagio na Italy.
  • Lambar karramawa na Chevalier de la Légion d'Honneur Francaise (Knight of the French Legion of Honor) 2003.
  • Lambar karramawa na Commandeur de l'Ordre National du Mérite, France, 1999.
  • Lambar karramawa na jami'ar Uppsala Janairu 2005.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. http://www.uu.se/en/about-uu/traditions/prizes/honorary-doctorates/theology/%7Ctitle=Honorary Doctors of the Faculty of Theology - Uppsala University, Sweden|website=www.uu.se|language=sv|access-date=2017-02-17}}