People's Health Movement
People's Health Movement | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Mulki | |
Hedkwata | Cape Town |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2000 |
phmovement.org… |
Ƙungiyar Lafiya ta jama'a (PHM). Cibiyar sadarwa ce ta duniya ta masu fafutuka kiwon lafiya, ƙungiyoyin farar hula da Kuma cibiyoyin ilimi musamman daga Kasashe masu tasowa. PHM a halin yanzu tana da tushe a cikin kasashe sama da saba'in 70 waɗanda suka haɗa da mutane da kuma ƙwararrun ƙungiyoyi tare da tsarin mulkin su. Kungiyar tana da ressa a Kudancin Asiya (India, Bangladesh, Sri Lanka), Afirka (Afirka ta Kudu), Pacific (Australia), Amurka ta Kudu (Brazil, Ecuador), Amurka ta Tsakiya (El Salvador, Nicaragua, Guatemala), Amurka ta Arewa (Amurka, Kanada), Turai (Italiya, Switzerland, Burtaniya, Girka) da sauran ƙasashe da yawa. PHM tana aiki don sake farfado da Kula da Lafiya ta a matakin Farko (PHC), kamar yadda aka bayyana a cikin Alma-Ata Declaration na shekarar 1978. [1]
"Daidaito, ci gaba mai dorewa da muhalli da zaman lafiya suna cikin muradin hangen nesa domin samun ingantacciyar duniya - duniya inda rayuwa mai lafiya ga kowa gaskiya ce; duniya da ke girmamawa, godiya da kuma murna da duk rayuwa da bambancin; duniya da ta ba da damar furewar baiwa da iyawar mutane don wadatar da juna; duniya inda muryoyin mutane ke jagorantar yanke shawara da ke tsara rayuwarmu...."
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Alma-Ata Declaration" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2012-06-27. Retrieved 2024-09-10.