Rafton Pounder
Rafton John Pounder (13 ga Mayu 1933 - 16 Afrilu 1991) ɗan majalisa ne a Pro-Assembly Unionist da kuma jam'iyyar Conservative Westminster MP daga Arewacin Ireland.
An haife shi a Ballynahatty, Shaw's Bridge, Belfast, ɗa ne ga Cuthbert C. Pounder, Rafton Pounder ya yi karatu a Makarantar Rockport, Charterhouse sannan kuma a Kwalejin Christ, Cambridge, inda ya kasance Shugaban Ƙungiyar Conservative Association (CUCA). [1]
An zabe shi matsayin dan majalisa na Westminster don wakiltar mazaɓar Belfast ta Kudu a zaben fidda gwani na 1963, kuma ya yi aiki har zuwa Fabrairu 1974 lokacin da ya sha kayi a matsayin Pro-Assembly Unionist ga Reverend Robert Bradford na United Ulster Unionist Coalition. Pounder ya kasance har wayau ɗan Majalisa a Tarayyar Turai daga 1973 zuwa 1974. Daga 1964 zuwa 1967, ya zama sakataren jam'iyyar Ulster Unionist Parliamentary Party.[2]
Ya auri Valerie Isobel ('yar Robert Stewart MBE), suna da ɗa ɗaya, Aidan, da diya ɗaya tare, Helen, ya zauna a Groomsport, County Down, har zuwa mutuwarsa a lokacin yana da shekaru 57. Ya rasu ya bar jikoki, Charlotte, Kate, Iona da Penelope.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Cambridge University Conservative Association". Archived from the original on 2007-03-14. Retrieved 2022-07-20.
- ↑ John F. Harbinson, The Ulster Unionist Party, 1882-1973, p.182
Tushe Labari
[gyara sashe | gyara masomin]- Leigh Rayment's Peerage Pages [self-published source] [better source needed]
- Times Guide to the House of Commons February 1974
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Hansard 1803–2005: contributions in Parliament by Rafton Pounder
Unrecognised parameter | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |