Jump to content

Rahman Owokoniran

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rahman Owokoniran
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rahman Owokoniran tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Legas ne. An naɗa shi kwamishinan gidaje (2003) sannan kuma kwamishinan masarautu da kan iyaka (2006) a zamanin Bola Tinubu a matsayin gwamnan jihar Legas. Ya jagoranci kwamitin samar da kananan hukumomi ashirin da kananan hukumomi goma sha bakwai na jihar Legas. A halin yanzu ya zama sakataren jam’iyyar Peoples Democratic Party (Nigeria) bayan zaben da aka gudanar a Osogbo, jihar Osun kwanan nan.[1][2][3][4][5][6]

Haihuwa da Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Rahman Owokoniran a cikin gidan Alhaji ASB Owokoniran. Ya sami digirin digirgir na BA daga Jami'ar Washington ta Gabas, Cheney, Jihar Washington, Amurka sannan yayi Masters a fannin Public Administration a Jami'ar Gabashin Washington.

Sana'a da Siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Rahman Akanni Owokoniran shi ne sabon sakataren jam’iyyar PDP na Kudu maso Yamma. Amma ya kasance tun a Jamhuriyyar Najeriya ta biyu . Owokoniran na daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar Unity Party of Nigeria, UPN, a jam'iyar ya zama dan majalisar dokokin jihar Legas a shekarar 1983.[7][8][9] [10]

Ya zama shugaban jam'iyyar Congress for National Consensus, CNC. Ya koma Alliance for Democracy (Nigeria) AD, kuma an nada shi Shugaban Kwamitin Samar da Kananan Hukumomin Jihar Legas, wanda ya kirkiro LGAs ashirin da LCDAs goma sha bakwai. An nada shi kwamishinan gidaje (2003) sannan kuma kwamishinan kula da masarautu da kan iyaka (2006).[11][12]

Jigo ne a jam’iyyar Peoples Democratic Party (Nigeria) kuma ya taba zama Darakta Janar na yakin neman zaben Sanata Bola Ahmad Tinubu, Jimi Agbaje, Lamido, Atiku Abubaka, da dai sauransu. Ya kuma kasance tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas.[13][14][15][16][17]

  1. "How PDP will dislodge APC in south west 2023". vanguardngr.com. 2021-05-10.
  2. "South west PDP congress a victory bitter to swallow". hallmarknews.com. 2019-05-10.
  3. "Fgs popular for cluelessness lacks service delivery plan says owokoniran south west pdp Secretary". vanguardngr.com. 2019-05-10.
  4. "25000 apc members defect as accord party guber candidate steps down for jimi-agbaje". m.guardian.ng. 2018-05-10.
  5. "PDP southwest congress". today.ng. 2021-03-10.
  6. "743 delegates decide south west pdp zonal leaders today". today.ng. 2021-04-12.
  7. "full list of cleared candidates for pdp south west". thenationonlineng.net. 2019-05-10.
  8. "suspense in pdp as southwest congress holds today". vanguardngr.com. 2019-05-10.
  9. "owokoniran apc government is ineffective". newtelegraphng.com. 2019-05-10.
  10. "reasons i fell Out with tinubu In lagos rahman Owokoniran". vanguardngr.com. 2021-05-10.
  11. https://www.thisdaylive.com/index.php/2022/01/17/my-interest-is-to-unite-the-party-says-owokoniran/
  12. "ambodes supporters dump apc endorse". thecitizenng.com. 2019-05-10.
  13. https://www.sunnewsonline.com/tag/rahman-owokoniran/
  14. "Atikus allies regroup in lagos state". newsexpressngr.com. 2019-05-10. Archived from the original on 2022-11-19. Retrieved 2022-11-19.
  15. "sule-lamido-transform-nigeria". today.ng. 2019-05-10.
  16. "lagos orders tan to remove posters". m.guardian.ng. 2019-05-10.
  17. "elections crisis hits lagos pdp". today.ng. 2019-05-10.