Rajaâ Cherkaoui El Moursli
Rajaâ Cherkaoui El Moursli | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Salé, 12 Mayu 1954 (70 shekaru) |
ƙasa | Moroko |
Harshen uwa | Abzinanci |
Karatu | |
Makaranta |
Lycée Descartes (en) 1975) Baccalauréat scientifique (en) Joseph Fourier University (en) 1982) doctorate (en) : nuclear physics (en) Joseph Fourier University (en) 1979) DEA (France) (mul) : nuclear physics (en) Joseph Fourier University (en) 1978) Diplôme d'études universitaires générales (en) : physics (en) Mohammed V University (en) 1990) doctorate in France (en) : nuclear physics (en) |
Harsuna |
Larabci Abzinanci |
Sana'a | |
Sana'a | physicist (en) da researcher (en) |
Employers | Mohammed V University (en) (1982 - |
Kyaututtuka | |
Mamba |
The World Academy of Sciences (en) KM3NeT (en) |
Rajaâ Cherkaoui El Moursli (an haife ta a ranar 12 ga watan Mayun shekarar 1954) farfesa ce ta ƙasar Moroko a fannin ilimin kimiyyar nukiliya, a sashin kimiyya a Jami'ar Mohammad V na Rabat.
Ta lashe lambar yabo ta L'Oréal-UNESCO don Mata a Kimiyya don aikinta akan Higgs Boson.
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi El Moursli a garin Salé a shekara ta 1954. Ta sami digiri na farko a fannin lissafi a Lycée Descartes a Rabat.[1] Sai da ta yi jayayya da mahaifinta a lokacin don zama yarinya ƙarama da za ta bar kasar Morocco mai ra'ayin mazan jiya don kara karatu. Ta ce nasarorin da Neil Armstrong ya samu da kuma wani malamin makarantar sakandare ya karfafa mata gwiwa.[2] Daga nan ta tafi yin karatu a Grenoble a ƙasar Faransa inda ta sami digirin digirgir a fannin kimiyyar lissafi a Laboratoire de Physique subatomique et cosmologie wanda wani bangare ne na Jami'ar Joseph Fourier. A shekarar 1982 ta koma Rabat.[1] Sannan ta jagoranci ƙungiyar bincike don gwajin ATLAS a CERN.
A shekarar 2015 ta samu lambar yabo ta L'Oréal-UNESCO ga mata a fannin kimiya na yankin Afirka da ƙasashen Larabawa. Kyautar ta ba da gudummawar da ta bayar don tabbatar da kasancewar Higgs Boson. Wannan barbashi yana da alhakin ƙirƙirar mass. El Moursli ta haɓaka matakin binciken kimiyya da kiwon lafiya na kasar Morocco. Daga baya an yaba mata saboda ita ce ta farko da ta samu digiri a fannin ilimin likitanci. [3] Dave Charlton, mai magana da yawun ATLAS ta taya ta murna da lambar yabon data samu ta kuma ta ce "ATLAS na taya Farfesa Rajaâ Cherkaoui El Moursli murnar wannan babbar lambar yabo, da kuma karramawar da ta yi wajen gano Higgs boson" [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Biography R. Cherkaoui Archived 2015-04-10 at the Wayback Machine, Mohammed V University, Rabat, retrieved 4 April 2015
- ↑ Rajaâ Cherkaoui El Moursli, an exceptional scientific career that started in Grenoble Archived 2015-04-09 at the Wayback Machine, 18 March 2015, Grenoble University, retrieved 4 April 2015
- ↑ 2015 L'Oréal-UNESCO For Women in Science Awards Archived 2015-11-17 at the Wayback Machine, Arnold Nou, 2 April 2015, WomenOfChina.cn, retrieved 4 April 2015
- ↑ http://home.cern/about/updates/2015/03/atlas-physicist-wins-loreal-unesco-women-science-award%7C Archived 2018-09-29 at the Wayback Machine ATLAS physicist wins L'Oreal-UNESCO Women in Science award