Rebecca Joshua Okwaci ‘yar siyasa ce'yar kasar Sudan ta Kudu, kuma ‘yar majalisa ce kuma babbar mai shigar da kara a jam’iyyar SPLM mai mulki a majalisar dokokin kasar ta wucin gadi har zuwa shekarar 2022. Ta kasance tsohuwar ministar sadarwa da aiyuka a waya sannan kuma tsohuwar ministar tituna da gada a gwamnatin Sudan ta Kudu. Ita ce "kwararriyar mai fafutukar neman zaman lafiya ce kuma mai bada shawarwari ga gudummawar da mata ke bayarwa a harkar zaman lafiya",[1] kuma ta kasance memba a wasu ƙungiyoyin mata na Sudan, Sudan ta Kudu ko na Afirka ta Kudu, ciki har da zama Sakatare-Janar na Matakan Ci Gaba. A cikin Disamba 2013, Jess Mathias na jaridar The Guardian ya bayyana ta a matsayin abin koyi ga mata matasa da ta zarce matan da ake kallonsu a matsayin madubi irin su Rihanna da Beyoncé . [1]
Okwaci ta sami digiri na farko a cikin harshen Ingilishi, adabi, da fassara daga Jami'ar Alexandria ta Masar, sannan kuma ta sami digiri na biyu a fannin haɓaka sadarwa daga Jami'ar Daystar ta Kenya.
Okwaci, a lokacin yakin basasar Sudan na biyu a shekarar 1986, ta shiga sabuwar kungiyar 'yantar da jama'ar Sudan da aka kafa kuma ta fara aiki a matsayin 'yar jarida a gidan rediyon SPLA, inda ta yi suna "muryar juyin juya hali".