Richard Acheampong
|
| |||||||
7 ga Janairu, 2021 - District: Bia East Constituency (en) Election: 2020 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2017 - District: Bia East Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017 District: Bia East Constituency (en) Election: 2012 Ghanaian general election (en) | |||||||
| Rayuwa | |||||||
| Haihuwa | Yankin arewa maso yamma, 18 Mayu 1970 (55 shekaru) | ||||||
| ƙasa | Ghana | ||||||
| Karatu | |||||||
| Makaranta | Kwalejin Nazarin Gudanarwa ta Jami'ar Digiri a kimiyya : Albarkatun dan'adam | ||||||
| Harsuna | Turanci | ||||||
| Sana'a | |||||||
| Sana'a |
ɗan siyasa, Ma'aikacin banki da operations manager (en) | ||||||
| Imani | |||||||
| Addini | Kiristanci | ||||||
| Jam'iyar siyasa |
National Democratic Congress (en) | ||||||
Richard Acheampong (an haife shi a watan Mayu 18, 1970) ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na Majalisar Bakwai na Jamhuriyyar Ghana ta Huɗu mai wakiltar Mazaɓar Bia ta Gabas a Yankin Yamma a kan tikitin Jam'iyyar Democratic Congress. [1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Acheampong a ranar 18 ga Mayun shekarar 1970. Ya fito ne daga Adabokrom, wani gari a Yankin Yammacin Ghana . [2] Ya shiga Kwalejin Gudanarwa na Jami'ar Kumasi a shekarar 2011 kuma ya sami digiri na farko a kan Human Resource. Ya kuma halarci Kwalejin Jami'ar Mountcrest, Kanda-Accra a 2016 kuma ya sami digiri na farko a fannin shari'a. [3]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Acheampong ma'aikacin banki ne. Ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin manaja a Nfana Rural Bank Sampa
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Acheampong memba ne na National Democratic Congress (NDC). A shekarar 2012, ya tsaya takarar neman kujerar Bia ta Gabas a kan tikitin jam'iyyar NDC ta shida a jamhuriya ta huɗu kuma ya yi nasara. [2]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Acheampong Kirista ne (Assemblies of God Church). Yana da aure (mai 'ya'ya biyar).[4]
Rigima
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Afrilun shekarar 2017, babbar hukumar Burtaniya a Ghana ta zargi Acheampong, George Boakye, Johnson Kwaku Adu, da Joseph Benhazin Dahah da taimakawa ƴan uwansu shiga Burtaniya ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar amfani da fasfo din diflomasiyya. Ya yi amfani da fasfo dinsa na diflomasiyya don samun takardar bizar hutu ga matarsa don hutun makonni biyu, ya ci gaba da zama a Burtaniya sama da shekara guda. [5] [6] [7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ghana MPs - List of MPs". GhanaMps. Retrieved 2019-02-15.
- 1 2 "Ghana MPs - MP Details - Acheampong, Richard". GhanaMps. Retrieved 2020-02-06.
- ↑ "Acheampong, Richard". Ghana MPS (in Turanci). Retrieved 2022-08-04.
- ↑ "Parliament of Ghana". Parliament Of Ghana. Retrieved 2024-09-25.[permanent dead link]
- ↑ "U.K. Accuses 4 Ghanaian MPs of Visa Fraud". Face2Face Africa (in Turanci). 2017-04-28. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "Four MPs barred from the UK for 'visa fraud'". Citi 97.3 FM - Relevant Radio. Always (in Turanci). 2017-04-26. Archived from the original on 2023-05-25. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "4 MPs Busted For VIsa Fraud". DailyGuide Network (in Turanci). 2017-04-27. Retrieved 2022-02-04.