George Boakye (dan siyasa)
George Boakye (dan siyasa) | |||
---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2009 - 6 ga Janairu, 2013 District: Asunafo South Constituency (en) Election: 2008 Ghanaian general election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Yankin Brong-Ahafo, 6 Oktoba 1956 (68 shekaru) | ||
ƙasa | Ghana | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Kwame Nkrumah University of Science and Technology Bachelor of Arts (en) : Kimiyyar zamantakewa University of Cape Coast Master of Education (en) : educational planning (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da educational theorist (en) | ||
Imani | |||
Addini | Katolika | ||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
George Boakye dan siyasan Ghana ne wanda ya taba zama dan majalisa mai wakiltar mazabar Asunafo ta kudu.[1][2][3] A halin yanzu shi ne ministan yankin Ahafo.[4]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a ranar 6 ga watan Oktoba, Shekarar 1956. Ya fito daga Sankore wani gari a yankin Brong Ahafo na Ghana. Ya samu digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Zamani a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah a shekarar 1992. Ya kuma sami digiri na biyu a fannin Ilimin Tsare-tsare da Gudanarwa daga Jami'ar Cape Coast a 2001.[1]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Masanin Ilimi ne. Ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kwalejin horas da jami’ar St. Joseph da ke Bechem kafin shiga siyasa.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Shi mamba ne na New Patriotic Party. Ya kasance Hakimin gundumar Asunafo ta Kudu.[1][5] Ya zama dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Asunafo ta kudu a yankin Brong Ahafo na kasar Ghana a watan Janairun 2009 bayan ya lashe zabensa a babban zaben Ghana na shekara ta 2008 da kuri'u 16,574 daga cikin kuri'u 32,953 masu inganci.[1][6] Eric Opoku na NDC ne ya gaje shi.[5]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Yana da aure da ‘ya’ya shida. Ya bayyana a matsayin Kirista kuma memba na Cocin Katolika.[1]
Rigima
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin watan Afrilun, shekarar 2017, Hukumar Burtaniya a Ghana ta zargi Boakye, Johnson Kwaku Adu, Richard Acheampong, da Joseph Benhazin Dahah da taimakawa 'yan uwansu shiga Burtaniya ba bisa ka'ida ba ta hanyar amfani da fasfo din diflomasiyya. Boakye ya nemi biza wa kansa da diyarsa daga baya ya bar ta a kasar Ingila wacce ta zauna tsawon shekaru 3 kafin ya koma Ghana.[7][8][9][10]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Ghana MPs – MP Details – Boakye, George". ghanamps.com. Retrieved 4 July 2020.
- ↑ Online, Peace FM. ""I Regret Being A Politician"". Peacefmonline.com – Ghana news. Retrieved 4 July 2020.
- ↑ "Former MP fights British High Commission". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 4 July 2020.
- ↑ "7 people electrocuted, 5 others injured at Amanfrom - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). Retrieved 2021-05-17.
- ↑ 5.0 5.1 "Former MCE responsible for my attack – Eric Opoku". www.ghanaweb.com (in Turanci). 4 April 2018. Retrieved 4 July 2020.
- ↑ AfricaNews (2 April 2017). "Ghana: UK blacklists 3 serving lawmakers over visa fraud". Africanews (in Turanci). Retrieved 4 July 2020.
- ↑ "U.K. Accuses 4 Ghanaian MPs of Visa Fraud". Face2Face Africa (in Turanci). 2017-04-28. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "Four MPs barred from the UK for 'visa fraud'". Citi 97.3 FM - Relevant Radio. Always (in Turanci). 2017-04-26. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ Boakye-Yiadom, Nana; Searcey, Dionne (2017-04-27). "Britain Accuses Ghana Lawmakers of Visa Fraud". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "4 MPs Busted For VIsa Fraud". DailyGuide Network (in Turanci). 2017-04-27. Retrieved 2022-02-04.