Rilwanu Adamu Jumba
2010 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | 1970 (54/55 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Sana'a | |||
Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu sarki ne a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeria. An haife shi a shekara ta (1970) a jihar Bauchi. An nada shi sabon sarkin Bauchi a shekara ta dubu biyu da goma (2010) bayan rasuwan mahaifinsa wato Alhaji Suleiman Adamu.[1][2]

Ya karanci kimiyyar Gina-gine a Jami'ar Tarayya na Tafawa balewa dake nan a cikin garin Bauchi a shekarar 1966 da kuma 2001 Sannan kuma yayi aiki da Nigerian port Authority na wasu shekaru. Sarkin na yanzu shine Amirul Hajji mafi dadewa a Bauchi wanda ya kula da ayyukan hukumar alhazai tsawon shekaru. Sarki Rilwanu mai ba da shawara ne kan mahimmancin samun katunan zabe wanda ke da mahimmanci wajen zabar shugabanni nagari. Ya fito fili ya fadakar da mutane akan muhimmancin tsafta da ke hana yaduwar cututtuka a cikin Al'umma gaba daya. Sarkin Bauchi ya ja kunne ga iyaye da su sanya ‘ya’yansu a makarantun addini da na kasashen yamma watau boko domin inganta rayuwarsu nan gaba. Mai martaba yana da kyauta mai girman gaske, inda yake baiwa matasa wadanda su ne kamar ƙashin bayan al’umma fifiko wajen samun sana’o’in dogaro da kai da rashin dogaro da ayyukan gwamnati. Ga Kirista ko Musulmi masu aminci da suka kai masa ziyara a lokacin bukukuwan Sallah, yana yi musu wa'azin bisharar zaman lafiya mai mahimmanci ga ci gaba.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.voahausa.com/a/nadin-sabon-sarkin-bauchi/1371956.html
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/news/2010/07/100729_emir
- ↑ https://guardian.ng/opinion/emir-of-bauchi-a-leader-worthy-of-emulation/