Ronald Chagoury
Appearance
Ronald Chagoury | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Najeriya, 8 ga Janairu, 1949 (75 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Mazauni | Lagos, |
Karatu | |
Makaranta | California State University, Long Beach (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa |
Ronald Chagoury (an haife shi ranar 8 ga watan Janairu, 1949) ɗan kasuwa ne kuma ɗan Najeriya, wanda ya kafa (tare da ɗan'uwansa hamshakin attajirin nan Gilbert Chagoury ), kuma Shugaba na kamfanin Chagoury Group.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ronald Chagoury a Najeriya a ranar 8 ga watan Janairun 1949, ɗan Ramez da Alice Chagoury, wadanda suka yi hijira daga ƙasar Lebanon a shekarun 1940. Ya yi karatu a College des Frères Chrétiens a Lebanon, kuma ya yi karatun kasuwanci a Jami'ar Jihar California, Long Beach, Amurka.[1]
Sunan Chagoury ya bayyana a cikin Panama Papers.[2]
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Chagoury ya auri Berthe, kuma suna da yara biyu.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Executive Team". Chagoury Group. Archived from the original on 2016-05-22. Retrieved 2016-05-20.
- ↑ Leaf, Aaron. "Nigeria's Chagoury Group Named In Latest Panama Papers Revelation Okayafrica". Okayafrica.com. Retrieved 2016-05-20.