Rosa Keleku
Appearance
Rosa Keleku | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | mace |
Ƙasar asali | Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango |
Suna | Rosa |
Shekarun haihuwa | 16 ga Janairu, 1995 |
Wurin haihuwa | Kinshasa |
Sana'a | taekwondo athlete (en) |
Wasa | Taekwondo |
Participant in (en) | 2016 Summer Olympics (en) da taekwondo at the 2016 Summer Olympics (en) |
Rosa Keleku (an haife ta ranar 16 ga watan Janairun Shekara ta 1995) ƙwararriyar ƴar wasan taekwondo ce ta Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo.
A gasar Afrika ta shekarar ta 2015, ta samu lambar azurfa a nau'in kilogiram 49. Ta samu gurbin shiga gasar Olympics ta bazara ta shekarar ta 2016 kuma ta ɗauki tutar ƙasarta a bikin buɗe gasar a Rio de Janeiro. Ita ce ɗaya tilo a cikin tawagar ƙasarta da ta tsallake zuwa gasar. Sauran mambobin tawagar ƙasarta an zaɓo su ne a ƙarƙashin wata ƙa'ida ta duniya.[1] Ta fafata a tseren kilogiram 49 na mata, inda ta sha kashi a hannun Itzel Manjarrez a wasan share fage.[2]