Jump to content

Rose Lokissim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rose Lokissim
Rayuwa
Haihuwa Cadi, 1953
ƙasa Cadi
Mutuwa Ndjamena, 15 Mayu 1986
Yanayin mutuwa  (extra-judicial killing (en) Fassara)
Karatu
Harsuna Larabci
Faransanci
Sana'a
Sana'a Soja
Aikin soja
Fannin soja Chadian National Armed Forces (en) Fassara

Rose Lokissim (an haife ta a shekarar  c. 1955 – ta rasu a ranar 15 ga watan Mayu, 1986) tana ɗaya daga cikin fitattun sojoji mata daga Chadi . Ta yi yaƙi da mulkin kama karya na Hissène Habré a cikin shekarar 1980s.

Rundunar ‘yan sandan ciki da aka fi sani da Documentation and Security Directorate (DDS) sun taɓa cafke ta yayin da take fasakwaurin takardu don ba wa 'yan tawayen da suka yi adawa da Habre. An kawo ta zuwa La Piscine sannan daga baya aka sauya mata sanannen gidan yarin da aka fi sani da Les Locaux . A shekarar 1984 aka dauke ta zuwa sel "C". Wannan ɗakin da ba shi da taga kuma mara kyau wanda ake kiransa da "ɗakin mutuwa" saboda kowace rana fursunoni suna mutuwa a wurin. Da farko an saka ta a ɗakin maza tare da wasu maza 60. Sannan daga baya aka sanya ta a na mata na wani ɗan gajeren lokaci, amma bisa damuwa da taraddadin neman tserewar ta, sai aka sake mai da ita cikin ɗakin maza. Ta kasance a wurin har tsawon watanni takwas. Lokacin da ta dawo cikin ɗakin matan, an ba da rahoton cewa ta ƙazantu sosai, jikinta duk datti ga kuma wari, kwarkwata ta lulluɓe ta ta ko'ina, gashin kanta kuwa duk ya hargitse. A lokacin da take Les Locaux, ta taimakawa fursunonin wajen fitar da wasiƙun su a boye zuwa ga danginsu. An azabtar da ita kan hakan kuma daga karshe aka kashe ta.

Rose Lokissim ta girma ne a gidan yawa a wani ƙaramin ƙauye a Chadi. An bayyana Rose a matsayin mace mai son taushin zuciya da son zaman lafiya. Ba ta bar shekarunta ko jinsi sun ruɗeta ga fadawa cikin hanyar gurbacewa ba yayin da ta tsinci kanta a yanayi ko hali na tsananin buƙata a kowane hali. Daya daga cikin dangin ta ya ba da labarin wani lokaci a shekarar 1967 da cewa mahaifin Rose na sauraren ta ne kawai yayin da yayi faɗa da ɗaya daga cikin matansa.