Jump to content

Ross Garland

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ross Garland
Rayuwa
Haihuwa 26 ga Yuni, 1974 (50 shekaru)
Karatu
Makaranta Brasenose College (en) Fassara
Durban High School (en) Fassara
Pembroke College (en) Fassara
Sana'a
Sana'a cricketer (en) Fassara
Kyaututtuka

Ross Garland (an haife shi a watan Yuni 26, 1974) ɗan fim ɗin Afirka ta Kudu ne kuma wanda ya kafa kamfanin samarwa Rogue Star Films.[1] Ya samar da fina-finai da suka haɗa da Confessions of a Gambler,[2] Big Fellas, U-Carmen eKhayelitsha, [1] da Spud . [1] Ya lashe kyautar zinare don Mafi kyawun Fim a Bikin Fina-Finan Duniya na Berlin a 2005.

Ya halarci makarantar sakandare ta Durban kuma ya yi karatu a Jami'ar Oxford, Kwalejin Brasenose, a matsayin Scholar Rhodes, kuma yana da digiri a fannin Drama, Psychology da Law. Ya buga wasan kurket na aji na farko a wasanni 12 don Kulob din Cricket na Jami'ar Oxford . [3]

Bayan ya sshafe lokaci a birnin New York na ƙasar Amurka a shekara ta 2001, ya koma ƙasarsa ta Afirka ta Kudu, inda ya yi aiki a matsayin lauya a Cape Bar, a Cape Town, Afirka ta Kudu har ya koma Australia a 2016 inda a halin yanzu yake zaune.

  1. Simon, Alissa (22 December 2007). "Review: 'Confessions of a Gambler'". Variety (in Turanci). Retrieved 9 April 2016.
  2. Ross Garland at CricketArchive