Saidu Dansadau
Saidu Dansadau | |||||
---|---|---|---|---|---|
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 District: Zamfara Central
1999 - 2003 District: Zamfara Central | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Jihar Zamfara, 20 ga Yuni, 1953 (71 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa |
All Nigeria Peoples Party All Peoples Party (en) |
Saidu Muhammed Dansadau (an haife shi a ranar 20 ga watan Yuni, 1953) an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltarmazabar Zamfara ta Tsakiya ta Jihar Zamfara, Nijeriya a farkon Jamhuriya ta huɗu ta Nijeriya, yana tafe a kan dandalin All People Party (APP). Ya kuma kan hau karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu shekarar 1999. An kuma sake zaben shi a watan Afrilu shekarar 2003 a kan jam'iyyar All Nigeria People's Party na tsawon shekaru hudu.
Haihuwa da farkon aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Dansadau a watan Yunin 1953. Ya sami B.Sc (Ilimi) da PGD (Gudanar da Jama'a), kuma yayi aiki a matsayin malamin ilimantarwa. Ya kuma fara matsakaici, sannan daga baya ya yi noma mai yawa a shekarar 1977, kuma ya ci gaba da kasancewa cikin harkar noma a duk lokacin da yake siyasa. Ya kasance Sakataren jam'iyyar na kasa (NPN) na jihar Sakkwato daga shekarar 1981 zuwa shekarar 1983 a lokacin Jamhuriyyar Najeriya ta biyu
Aikin majalisar dattijai
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan ya hau kujerarsa a majalisar dattijai a watan Yunin shekarar 1999, an nada Dansadau a kwamitocin kula da Asusun Jama'a, Kiwon Lafiya, Kwadago, Kasuwanci (shugaban), Tsare-tsaren Kasa da Harkokin Cikin Gida. Shekaru da dama ya kasance Babban Sakatare na Kungiyar Sanatocin Arewa. A watan Maris na shekarar 2005 Dansadau ya kuma yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Cif Adolphus Wabara, da ya yi murabus tunda yana da hannu a badakalar cin hancin Naira miliyan 55. A watan Afrilu na shekarar 2005 Wabara ya yi murabus daga karshe bayan zargin da aka yi cewa shi da wasu sun karbi cin hancin $ 400,000 daga ministan ilimi, Fabian Osuji.