Saleh Al-Talib

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Saleh Al-Talib
Rayuwa
Haihuwa Riyadh, 23 ga Janairu, 1974 (50 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Islamicist (en) Fassara, Liman, khatib (en) Fassara da mai shari'a
Imani
Addini Musulunci

Sheikh Saleh bin Mohammed Al Talib (an haife shi ranar 23 ga Janairun 1974) a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. malamin Saudiyya ne, mai wa’azi, Limami, Khatib kuma alkali.[1] mutum ne mai hazaka da kuma mai karatun Alkur'ani ne kuma mai wa'azi.

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kammala karatunsa na firamare da sakandare yayi digiri na farko a jami’ar Imam Saud da ke Riyadh inda ya ci gaba da yin digiri na biyu a fannin shari’ar Musulunci da kuma shari’a a Georgetown, Washington DC, Amurka. Ya kuma yi sa'ar samun takardar shedar karatu "A wurin mutum goma" Kamar irinsu Sheikh Mahmoud Omar Sukkar, Saber Hassan Abu Sulaiman, da Abdul Halim Saber Abdul Razak. Ya kuma samu goyon baya da taimako daga Shaykh Abdul Aziz bin Abdullah bin Baaz da Saleh bin Abdul Aziz Al-Sheikh, Ministan Harkokin Addinin Musulunci, da Janar Mufti na Saudiyya.[2] Kasancewar yana da gogewa da kwarewa wajen aiwatar da ayyukan shari'a a Kotun Koli a Riyadh  tare da manyan Shehunai kamar Abdul Aziz bin Ibrahim Al-Qasim, Abdullah bin Abdul Aziz, shugaban kotun Al Taif, An nada Sheikh Talib a hukumance a wurin da ake so na wani alkali a babbar kotun Makkah, wurin da ya dace.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]