Jump to content

Sam Uzochukwu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sam Uzochukwu
Rayuwa
Haihuwa 23 ga Afirilu, 1940 (84 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Lagos
Sana'a
Sana'a literary critic (en) Fassara da Malami
Employers Jami'ar jahar Lagos

Sam Uzochukwu malami ne ɗan Najeriya kuma masani kan waƙoƙin baka na ƴan ƙabilar Igbo.[1]

An haifi Uzochukwu a shekarar 1940 a Ebenato, karamar hukumar Nnewi ta kudu, jihar Anambra, Najeriya. Bayan ya yi Digiri na biyu a Harshen Turanci daga Jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife (1966), ya koma Nazarin Igbo.[2] Uzochukwu ya samu digirin digirgir ne a jami’ar Legas a shekarar 1981 inda ya karanci adabin baka na Igbo. Ya zauna a Jami’ar Legas, inda ya zama Farfesa kuma Shugaban Sashen Nazarin Afirka da Asiya.

Ya yi aiki wajen tattarawa da rubuta waƙoƙin baka na Igbo, musamman wakokin jana'iza, kuma ya wallafa ayyukan kirkire-kirkire da na ban mamaki a harshen Igbo.[1] An wallafa Festschrift-(littafin girmamawa) domin shi a shekarar 2008.[3]

Uzochukwu shi ne Farfesa na farko a duk faɗin Mbanese - wanda shine babban sunan gamayyar al'ummomi biyar (cikin goma) da suka haɗa da karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra. Waɗannan al’ummomin sune Ebenato, Ezinifite, Akwaihedi, Osumenyi da Utuh.[4] A shekarar 2019, Farfesa Sam ya ƙaddamar da Gidauniyar Ilimi mai zurfi, sannan kuma ya bayyana tarihin rayuwarsa mai taken A Single Palmnut[5]

  • Mbem Akwamozu [Funeral Dirges], 1985. 08033994793.ABA
  • Akanka, Na Nnyocha Agumagu Igbo [Criticism of Igbo Poetry], 1990 08033994793.ABA
  • Abu Akwamozu [Songs of Mourning], 1992 08033994793.ABA
  • Traditional funeral poetry of the Igbo, 2001 08033994793.ABA
  • Traditional birth poetry of the Igbo, 2006 08033994793.ABA
  • A Single Palmnut, The Autobiography of Prof. Samuel Udezuligbo Uzochukwu, 2019.
  1. 1.0 1.1 Ernest Emenyonu, "Ugochukwu [sic], Sam", in Simon Gikandi, ed., Encyclopedia of African Literature, Routledge; 2002. 08033994793.ABA. Online version
  2. 'Traditional Elegiac Poetry of Igbo: A study of the major types'. PhD Thesis, University of Lagos, 1981. See Helen Chukwuma, Igbo oral literature: theory and tradition, 1994, p.9
  3. Iwu Ikwubuzo, Chinyere Ohiri-Aniche and Chigozie Nnabuihe, eds., Udezuluigbo: a festschrift in honour of Sam Uzochukwu, 2008. 08033994793.ABA.
  4. Okafor, Izunna. "Ebenator First Professor Launches Edu. Foundation". www.echonigeria.com (in Turanci). Archived from the original on Jul 7, 2022. Retrieved 8 June 2023.
  5. Izunna Okafor "Mabnese 1st Professor Launches Edu. Foundation, Unveils Autobio", The Nigerian Voice 17 October 2019. Retrieved 22 November 2019.